Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-10 14:24:26    
Ya fi kyau mutane masu fama da ciwon sukari su ci bakar cakulan da blueberry

cri
Bisa rahoton nazari da kwalejin Karolinska ta kasar Sweden ta bayar, an ce, bakar cakulan da dan itace wanda ake kiransa blueberry a bakin Turawa abinci ne da ke iya kiyaye lafiyar jiki ga mutane masu fama da ciwon sukari.

Kuma rahoton ya bayyana cewa, manazarta sun sa wasu mutane masu fama da ciwon sukari da aka gudanar da bincike gare su bisa son rai su dandana farar cakulan da bakar cakulan da kuma cakulan da ke kunshe da madara. Daga baya kuma sakamakon binciken ya bayyana cewa, jimlar yawan sukari da ke cikin jininsu ta karu sakamakon cin farar cakulan da kuma cakulan da ke kunshe da madara, amma wannan jimla ba ta samu canjawa sosai ba ga wadanda suka ci bakar cakulan. Ban da wannan kuma, manazarta sun sa mutane 10 da ke fama da ciwon sukari da kuma mutane 10 da ke da lafiya jiki su sha ruwan blueberry, daga baya kuma an gano cewa, jimlar yawan sukari da ke cikin jininsu ba ta samu karuwa a bayyane ba.

Mr. Purisima, kwararre ne a fannin ciwon sukari kuma babban malami na kwalejin Karolinska ya bayyana cewa, yiyuwar kamuwa da ciwon sukari tana ta karuwa a kasar Sweden har ma a duk duniya, shi ya sa neman samun abincin da ke cancantar masu fama da ciwon ya zama wani batu ne da ya jawo hankalin sashen ilmin likitanci.

To, masu sauraro, yanzu sai ku shakata kadan, daga baya kuma za mu ci gaba da yin muku wani bayani kan ciwon sukari.

Bisa wani sabon nazarin da kasar Amurka ta gudanar, an ce, mutane masu fama da ciwon sukari da ke da kiba sun fi saukin kamuwa da ciwon zuciya. Haka kuma yiyuwar kamuwa da ciwon zuciya ga mata masu fama da ciwon sukari da ke da kiba tana kaiwa kusan kashi 80 cikin kashi dari yayin da wannan jimla take kaiwa kusan kashi 90 cikin kashi dari ga maza.

Madam Caroline da dai sauran kwararru na cibiyar nazarin zuciya da huhu da kuma jini ta kasar Amurka sun ba da rahoto a kan mujallar 'yi wa masu fama da ciwon sukari jiyya' ta kasar Amurka, cewar kullum ba a iya raba kiba da ciwon sukari ba, mutane masu fama da ciwon sukari sun fi saukin kamuwa da ciwon zuciya, kuma samun kiba fiye da kima ya kara irin wannan hadari.

Manazarta sun gudanar da bincike ga mutane fiye da 3400 cikin dogon lokaci, daga baya kuma sakamakon binciken ya bayyana cewa, game da mata da shekarunsu suka zarce 50 da haihuwa, yiyuwar kamuwa da ciwon zuciya ta kai kashi 34 cikin dari, kuma wannan jimla tana kaiwa kashi 55 cikin dari ga mutane masu fama da ciwon sukari wadanda ke da madaidaicin nauyin jiki sosai, amma wannan jimla ta iya kaiwa kashi 79 cikin dari ga mutane masu fama da ciwon sukari da ke da kiba fiye da kima. Game da maza kuma, wannan jimloli uku sun kai kashi 49 cikin dari da kashi 77 cikin dari da kuma kashi 87 cikin dari bi da bi.

Amurkawa suna fama da matsalar samun kiba fiye da kima. Bisa kididdigar da aka bayar, an ce, ya zuwa yanzu game da Amurkawa fararen fata da wadanda asalinsu Afirka da kuma Latin Amurka da shekarunsu suka zarce 50 da haihuwa, yawansu da ke da kiba ya zarce kashi 2 cikin kashi 3, a ciki yawansu da ke samun kiba fiye da kima sosai ya zarce sulusi. Kuma a cikin rahoton, manazarta sun nuna cewa, in ba a canja irin wannan halin da ake ciki ba, to ya zuwa shekara ta 2050, watakila yawan Amurkawa masu fama da ciwon sukari zai zarce miliyan 48.3, ta haka yawan mutanen da ke fama da ciwon zuciya da ke da nasaba da ciwon sukari zai samu karuwa sosai.

To, jama'a masu sauraro, shirinmu na yau na ilmin zaman rayuwa ke nan. Muna fatan kun ji dadinsa, da haka Kande da ta shirya muku wannan shiri kuma ke cewa a kasance lafiya.(Kande Gao)