Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-08 20:48:58    
Wasu labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri

---- Kwanan baya wakilinmu ya samu labari daga wajen ma'aikatar ilmi ta kasar Sin cewa, domin kara saurin tallafawar kwararrun mutane 'yan kananan kabilu wadanda suke kan matsayin ilmi na digiri mai daraja ta 3 da mai daraja ta 2, a shekara mai zuwa jami'o'in a duk kasar za su dauki dalibai 'yan kananan kabilu masu binciken ilmi mai zurfi, wadanda yawansu ya kai 4,700, daga cikinsu da akwai dalibai masu digiri mai daraja ta 2 3,700, da na digiri mai daraja ta 3 l,000.

An ce, a shekara mai zuwa za a dauki dalibai 'yan kananan kabilu masu binciken ilmi mai zurfi daga larduna da jihohi masu ikon tafiyar da harkokin kansu da biranen da ke karkashin gwamnatin tsakiya kai tsaye su 12 da ke yammacin kasar Sin, da lardin Hainan da rundunar soja masu aikin kawo albarka ta jihar Xinjiang, da yankunan kananan kabilu masu ikon tafiyar da harkokin kansu da ke larduna 4 wato lardin Hebei da na Liaoning da na Jilin da na Heilongjiang, da sauran wasu jami'o'I da kwalejoji na cikin kasar, musamman ma za a dauki dalibai masu bincike-bincike daga wajen mutane masu aikin bada ilmi da kimiyya da fasaha da likitanci da al'adu da sadarwa, da na fannonin tattalin arziki da makamashi da sauran harkokin rayuwar jama,a.

---- Kwanan baya, wakilinmu ya je wasu makarantu masu koyar da harsuna 2 da ke yankin kabilar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kansa na Diqing da ke lardin Yunnan na kasar Sin, inda suka ga 'yan makarantu suna koyon ilmin kabilar Tibet cikin nitsuwa, wannan ba ma kawai ya zama wani kyakkyawan halin da makarantun ke ciki ba, har ma za a iya cin gadon al'adun kabilar Tibet sosai.

Mr. Yang Hongbing, shugaban hukumar bada ilmi ta yankin kabilar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta Diqing da ke lardin Yunnan ya bayyana cewa, cikin shekaru da yawa da suka wuce, yankin Diqing ya yi kokarin tafiyar da aikin ba ilmi ta hanyar yin amfani da harsuna 2 wato harshen kabilar Han da na kabilar Tibet, shi ya sa aka gaji harshe da harufa na kabilar Tibet da kyau sosai, kuma an tallafawa kwararrun mutane da yawa domin raya jihar Tibet. Yanzu a duk yankin Diqing da akwai makarantu ko wuraren ba da ilmi 22 wadanda suke gudanar da aikin koyarwa ta harshen kabilar Tibet, yawan 'yan makaranta da suke koyon harshen kabilar kuma ya kai kusan 3,000.

Cikin 'yan shekarun da suka wuce, 'yan makaranta da ba na kabilar Tibet ba su ma suna ta kara nuna himma wajen koyon harshen kabilar Tibet.