Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-08 20:48:22    
Zamanin da da na yanzu da na nan gaba na mutanen Kucong

cri

Mutanen Kucong wani reshe ne na kabilar Lahu, wanda yake da mutane wajen dubu 30, yawancinsu suna zaune a kan shiyyar tuddai wadda tsayinta daga matsayin teku ya kai mita 1800 har zuwa 2100 da ke lardin Yunnan. A da sukan tafiyar da zama ne ta hanyar yin farauta da ciro 'ya'yan itatuwa da ke cikin daji, sabo da haka suna fama da wahala da yunwa.

A shekarar 2005, wani bayani mai lakabin "Har ila yau mutanen Kucong da ke gundumar Zhenyuan ta lardin Yunnan suna fama da talauci" ya jawo hankalin Mr. Wen Jiabao, firaministan kasar Sin sosai. A ranar da ya ga wannan bayani kuma ya mika muhimmin kuduri cewa, ya kamata a gudanar da manufar ba da taimako ga shiyyoyin kananan kabilu wajen yaki da kangin talauci, kuma a dauki kwararan mataikai ta yadda mutanen Kucong za su fid da kai daga zaman talauci cikin sauri.

A wannan shekara wato shekarar 2005, wata yarinya mai sunan Xu Lianfen, mutumiyar Kucong wadda take da shekaru 10 da haihuwa kawai, amma kudurin firaminista Wen ya haddasa manyan sauye- sauye ga zaman rayuwarta.

Yarinya Xu: "Tun shekaruna 2 da haihauwa, mahaifina ya rasu, lokacin da nake da shekaru 3 kuma mahaifiyata ta sake yin aure."

Wakiliyarmu: "Yaya sunan garinku?"

Yarinya Xu: "Yakou ne na kauyen Muchang da ke garin Zhedong, a can muhallin zama ba abin a zo a gani ba ne, kuma akan yi zaizayewar kasa da duwatsu."

Yanzu, yarinya Xu Lianfen ta yi kaura zuwa wani sabon gida na kauyen Fuxin da ke da nisan kilomita 8 a tsakaninsa da garin gunduma Zhenyuan, ita ma tana yin karatu cikin makarantar gundumar. Yanzu kuma da akwai mutanen Kucong wadanda yawansu ya kai 1,100 da suka yi kaura daga manyan tsaunuka zuwa wannan wuri.

(Murya ta 2 ta zancen da aka yi tsakanin wakilinmu da yarinya Xu)

"Yaya kike ji cikin makarantar?"

"Da kyau sosai, kuma ina farin ciki a kowace rana."

Malama Zhang Yan mai koyarwa ce ga 'yan karamar makarantar sakandare na mataki na 3 na gundumar Zhenyuan ita ma mutumiyar Kucong ce ta kabilar Lahu, kafin ta zama malamar koyarwa, ta taba yin karatu cikin babbar makarantar midil da kuma jami'a bisa taimakon kudi da ta samu daga wajen gwamnatin kasar da mutanen garinta. Ta ce, "Ni ma mutumiyar Kucong ce, garina yana shiyyar da ke cunkushe da mutunen Kucong. Kuma ni ce malamar farko da ta fito daga can, a lokacin da nake makaranta wato a shekarar 1989, babu 'yan mata da yawa da suka samu damar yin karatu, kuma 'yan mata da suka daina karatu suna da yawan gaske, manoma sukan hana 'ya'yansu mata su shiga makaranta."

Amma yanzu, harkar ba da ilmi ga mutanen Kucong ta samu manyan sauye-sauye, wannan ya faranta ranta kwarai, ta ce, "Na riga na shafe shekaru 12 ina aikin karantarwa, na gane wa idona sauye- sauye da yawa da mutanen Kucong suka samu. Yanzu a kauyenmu da akwai 'yan matan Kucong da yawa wadanda suka shiga makaranta, kuma an tabbatar da manufar samun ilmi tilas ga yawancin yaran Kucong na garinmu wadanda suke cikin makarantu masu tsarin karatu na shekaru 9, lalle wannan wani canji ne mai faranta ran mutane sosai."

An ce, matsalar samun bunkasuwa ta mutanen Kucong na kabilar Lahu kullum tana jawo hankali da kuma samun kulawa daga wajen gwamnatin kasar Sin. Tun bayan da firaminista Wen Jiabao ya mika kuduri a shekarar 2005 zuwa yanzu, daga shekarar 2006 kuma gwamnatin lardin Yunnan ita ma ta fara tafiyar da shirin shekaru 5 na bada taimako ga mutanen Kucong wajen yaki da talauci. Ba shakka wadannan mutane masu fama da talauci a zamanin da za su iya samu makoma mai kyau.