Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-04 16:27:06    
Zumuncin dake tsakanin kasar Sin da Pakistan zai dade

cri

Pakistan makwabciyar kasar Sin ce mai aminci, da akwai kyakkyawar dangantakar amincin dake kasancewa tsakanin kasashen nan biyu wajen yin mu'amala da hadin kai a fannonin siyasa da tattalin arziki da ciniki da kimiyya da ilmi da kuma al'adu.A shekara ta 2006 yayin da shugaban kasar Sin Hu Jintao yake bakuncin kasar Pakistan,ya kulla wata yarjejeniya da takwaransa na Pakistan na wannan lokaci Musharaff,a cikin yarjejeniyar an tanadi cewa kasashen biyu su aika wa juna da tawagar da ke kunshe da matasa dari ta kai ziyarar sada zumunta kowace shekara. A shekara ta 2007 matasan kasar Sin da Pakistan sun tabbatar da ziyararsu ta juna ta sada zumunta a karo na farko tare da nasara. A watan Augusta na wannan shekarar da muke ciki,wata kungiyar kasar Sin dake kunshe da matasa dari ta tafi Pakistan ta cigaba da sada zumunci a tsakanin kasashen nan biyu.

A ran 21 ga watan Augusta da yamma,kungiyar matasa ta kasar Sin ta isa birnin Karachi na kasar Pakistan dake bakin teku,daga nan ta fara ziyararta ta sada zumunta ta kwanaki takwas a kasar Pakistan.A daren wannan ranar bayan ta sauka,Mr Ishratul Ibad,gwamnan lardin Singhder ya shirya dina musamman domin kungiyar matasa ta kasar Sin wadda ta kawo ziyara.A cikin jawabinsa,Mr Ishratul ya yi maraba da zuwan kungiyar matasaa ta kasar Sin da hannu bibbiyu ya ce.

" Kome zai faru a duniya,kasar Sin ta cancanci amintacciyar aminiyar Pakistan har abada.na sanar muku cewa a duk lokacin da kuke ziyara,za ku iya jin zumuncin da mutanen Pakistan ke nuna wa mutanen kasar Sin." A cikin nata jawabi,shugabar kungiyar matasa ta kaar Sin kuma sakataren sakatariyar kwamitin tsakiya na kungiyar matasa mabiya kwaminisanci ta kasar Sin Madam Luo Mei ta yi fatan ziyarar juna ta fuskar aminci da matasan kasashen nan biyu ke yi za ta kara inganta zumuncin dake tsakanin matasa na Sin da Pakistan. Ta ce  "da zuciya daya nake fatan zumuncin al'ada dake tsakanin Sin da Pakistan zai ci gaba da yaduwa ta hanyar mu'amalar amin da matasan kasashen nan biyu suke yi tsakaninsu."

Pakistan kasa ce ta musulmi,a shekara ta 1947 ta sami yancin kanta daga mulkin mallaka na Britaniya da ke cikin kasar Indiya,wani yanki mai cin gashin kansa a kungiyar Common wealth,jagoran musulmi Mohammed Ali Jinah na wannan zamani shi ne gwamnan na farko,daga baya aka daukaka shi "uban kasar Pakistan". Ya rasu a shekara ta 1848 domin tunawa da shi, gwamnatin Pakistan ta gina wani kabari dominsa a Karachi,hedkwatar kasa na wannan lokaci.Wata rana da safe kungiyar matasa ta kasar Sin ta kai ziyarar ban girma a kabarin Jinah,ta kuma ajiye kambun furanni domin nuna girmamawa.Da suka sami labarin manyan fitilun da ake amfani da su a babban masallanci sun zo ne daga kasar Sin, matasa kasar Sin a filin sun yi farin ciki da ganin zumuncin dake tsakanin kasar Sin da Pakistan ya game a ko ina a kasar Pakistan.Wani dan kungiyar matasa ta kasar Sin kuma dalibi ne da ya zo daga jami'ar koyon ilimin kudade ta birnin Shanghai Li Chang ya bayyana cewa 

"yayin da muka ajiye kambun furanni a gaban kabarin marigayi Jinah,abu daya da aka kayatar da kabarin shi ne fitilu masu lu'u lu'un da kungiyar mabiya musulunci ta kasar Sin ta baiwa kasar Pakistan,Jinah,wani jagoransu ne mai girma da daukaka, a cikin kabarinsa da mutanen miliyoyi ke girmamawa da akwai fitilu masu lu'u lu'u da kungiyar musulunci ta kasar Sin ta bayar, a ganina babbar alama ce da ke shaida zumuncin da ketsakanin kasar Sin da Pakistan,wannan al'amari ya burge ni kwarai da gaske."

Bisa shirin da shugabani na kasashen nan biyu suka tsara,makasudin kai wa juna ziyara tsakanin matasa na Sin da Pakistan, shi ne samo magadan da suka ci gaba da bunkasa zumuncin dake tsakanin kasashen biyu.A cikin wannan lokacin ziyara matasan kasar Sin sun yi mu'amala da takwarorinsu na kasar Pakistan yadda ya kamata.


1 2 3