Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-02 22:13:39    
Wasu malaman da suka nuna jarumtaka sosai a cikin girgizar kasa ta lardin Sichuan

cri

Ran 10 ga wata rana ce ta malamai ta kasar Sin. A cikin ranar malamai ta shekarar da muke ciki, wasu mutane sun jawo hankalin mutane sosai, su ne malaman da suka nuna jarumtaka a cikin bala'in girgizar kasa ta lardin Sichuan. A cikin mummunar girgizar kasa da ta auku a ran 12 ga watan Mayu, sun kubutar da 'yan makaranta masu kananan shekaru da haihuwa ba tare da kulawa da zaman lafiyarsu na kansu ba, kuma dimbinsu sun rasa rayukansu. Kafin zuwan wannan ranar malamai, gwamnatin kasar Sin ta ba su lambobin yabo da kuma gayyatarsu wajen halartar bikin bude gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing. To, a cikin shirinmu na yau, za mu gabatar muku da wasu nagartattun malamai daga cikinsu.

Zhou Rulan wata malama ce mai koyar da Sinanci a makarantar firamare ta Hongyan ta birnin Pengzhou na lardin Sichuan. Bayan aukuwar girgizar kasa, ta kutsa kai cikin aji har sau hudu daya baya daya domin ceton yara. A karshe dai ita da shugaban makarantar sun kubutar da dukkan yara 52 na ajinta. Kuma Zhou Rulan ta bayyana cewa, a wancan lokaci, ba ta damu da kanta ko kadan ba, abin da ya tsoratar da ita shi ne yara su gamu da hadari. Kuma ta kara da cewa,

"A wancan lokaci, na ji tsoro kadan, wato idan dakuna sun lalace, to yara za su ji raunuka. Kuma ina ganin cewa, ya kamata na dauki alhakki kan zaman lafiyar yara, har ma ban taba kula da lafiyata ba, abin da ke cikin zuciyata shi ne tun da iyaye da makaranta da kuma zaman al'umma suka ba ni aiki na kula da wadannan yara, to ya kamata in dauki alhakki kan lafiyarsu."

Zhou Rulan da 'yan makaranta sun yi kokari sun kubutar da kansu daga hadarin, amma wasu malamai kuma sun rasa rayukansu yayin da suke ceton 'yan makaranta. Xiang Qian mai shekaru 21 da haihuwa wata malama ce mai koyar da Turanci a makarantar firamare ta Longju na birnin Shifang. Kafin aukuwar girgizar kasa, tana koyar da Turanci a bene na uku na ginin karatu. Bayan da ta kwashe 'yan makarata 37, ginin ya ruguje kwaram. Amma har ma a lokacin karshe na zaman rayuwarta, Xiang Qian ba ta manta da kare 'yan makaranta ba. Lokacin da sojoji masu ceton mutane suka gano gawarta a cikin kangaye, tana karewar 'yan makaranta uku a karkashin jikinta. Xiang Zhonghai, mahaifin Xiang Qian ya bayyana cewa, "Gudanar da aikin koyarwa burinta ne, amma ta riga mu gidan gaskiya har ma ba ta taya murnar ranar malamai ta farko a cikin zaman rayuwarta ba. A matsayina na wani mahaifi, ina bakin ciki sosai da mutuwarta, amma ta ba da misali ga malamanmu, shi ya sa ina jin alfahari sosai gare ta."

Lokacin da wadannan malamai jarumai da kuma iyalansu ke zantawa da wakilinmu, dukkansu sun ambaci kalmar "Alhakki". Malama Zhou Rulan ta bayyana cewa, a kewayensu, ana iya samun dimbin abokan aikinta da malamai da ba a san sunayensu ba, wadanda su ma suka bayar da gudummowa a gaban hadarin. Kuma ta kara da cewa, "A idona, a wancan lokaci, dukkan malamai sun sauke nauyin da aka dora musu, wato sun samar da yawan zarafofin samun rai ga 'yan makaranta a maimakon kansu. Kuma dukkan malamai sun dauki aniyar kwashe 'yan makaranta ba tare da kula da kansu ba. Kwaram ina ganin cewa, na ji alfahari sosai da na iya zama wata malama mai koyarwa."