Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-01 15:51:55    
Zaman jin dadi na iyalin manoma Wang Honglin da matarsa

cri
Wakar da kuka saurara dazu wata waka ce da madam Ma Xiuhua, wata manomiya wadda take zaune a jihar Ningxia ta kabilar Hui mai ikon tafiyar da harkokin kanta da ke arewa maso yammacin kasar Sin. Cikin shirinmu na yau za mu ja ku zuwa gidanta don jin yadda Madam Ma Xiuhua da mijinta Wang Honglin da sauran iyalinta suke gudanar da zaman nishadi a gidansu.

Wakilanmu sun dauki mota daga birnin Yinchuan, hedkwatar jihar Ningxia mai cin gashin kanta sun doshi kudu, sun shafe kusan rabin awa suna tafiya sai suka isa wani wuri inda suka ji haushin karnuka, nan ne kauyen da gidan Ma Xiuhua ya ke.

Da baki sun zo, sai mai gida Wang Honglin da iyalinsa su kama shan aiki, suna kama kifaye da yanka kaji da kuma debar kayan lambu domin nuna karamci ga bakin, ba da dadewa ba sai a gama dafa abinci, kuma a ajiye shi bisa kan tebur, ciki har da shinkafa da miya da sauran cimaka, dukkansu abincin musulmi ne sosai, madam Ma ta ce,

"Dukkan abincin da gidanmu ya sayar suna da halayen musamman na musulmi, bakin da suka zo ba don kome ba ne illa cin abincinmu kawai, sun ce abincin gidanmu yana da araha, kuma yana da dadi, sabo da haka bayan da suka ci abinci a karo na farko a nan, kuma yawancinsu za su sake dawowa."

Mr. Wang Honglin wani manomi ne da ke zaune a kauyen Taqiao na unguwar Xingqing ta birnin Yinchuan, a da ya dukufa kan aikin noma. Daga baya bisa karin himmar da ya samu daga wajen gwamnatin kasar wajen gudanar da sana'o'i da yawa, da samun arziki ta hanyar yin aiki tukuru, ya fara kiwon kifaye daga shekarar 1994. ya ce,

"Na samu labari ta talabijin cewa, yanzu yin fatsa da yin zaman nishadi cikin gidan manoma wata hanya ce mai kyau da ake bi wajen samun aikin yi. Kauyenmu kuma ya aike da mu zuwa sauran wurare na kasar Sin ciki har da lardin Shandong domin koyon fasahar tafiyar da wadannan ayyuka, muna gani cewa ma iya samun kudin shiga da yawa ta hanyar yin zaman nishadi cikin gidan manoma"

Madam Ma Xiuhua ita ma ba ta huta a gida ba, tana koyon fasahar kiwon kifaye daga wajen masanan kimiyya da fasaha. Bayan da Wang Honglin da matarsa suka shirya kome da kome, sun bude wani wurin yin fatsa da fara aikin nishadi na manoma musulmi daga watan Afrilu na shekarar da ta wuce. Bayan da ma'aikatan hukuma da manoman kauyen Taqiao suka ji labarin, dukkansu sun je gidansu don taya su murna, kuma sun nuna musu goyon baya wajen tunani sosai. Madam Ma Xiuhua ta gaya wa wakilanmu cewa,

"Da aka ji labarin budewar dakin yin nishadi na manoma musulmi a gidanmu da kuma kebe wurin yin fatsa, sai shugabannin gundumarmu da na kauyenmu dukkansu suka zo nan don taya mana murna, kuma sun nuna mana goyon baya, sabo da haka muka kara nuna amincewa ga gudanar da wannan aiki namu."

Yanzu a kowane karshen mako, mutane da yawa sukan je gidan Mr. Wang, inda suke yin fatsa, ko kuma suke rera wakoki da sauran wasannin nishadi, da kuma cin abincin musulmi, sabo da haka iyalan Mr. Wang suna shan aiki sosai a lokacin, amma duk da haka suna farin ciki sabo da kyakkyawan yabo da suka samu daga wajen bakin, ban da wannan kuma abun da ya fi faranta ran Mr. Wang shi ne, yanzu yawan kudin shiga da iyalinsu ke samu ya kai kusan Yuan 1,000 a kowace rana, ya ce,

"Yanzu lalle muna cikin zaman jin dadi sosai, wallahi! kamar aljanna muke ciki. Yanzu kuma dakunan da aka gina a kauyenmu suna da kyau sosai, yayin da dana ya yi aure, an gina masa dakuna daidai kamar na mutanen birni. Sharudan zaman rayuwa na iyalinmu suna da kyau, kusan a ce muna cin naman kifaye da na shanu da na awaki a kowace rana, yanzu ma har ba mu son cin namun dabbobin gida sosai, akasin haka kuma mun fi son cin dankalin turawa."

To, jama'a masu sauraro, mun dai kawo muku bayani mai lakabin haka, "Zaman jin dadi na iyalin manoma Wang Honglin da matarsa", yanzu sai ku dan shakata kadan, daga bisani kuma za mu dawo domin kawo muku wasu labaru.