Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-26 17:23:44    
'Yar wasan Piano Li Ang

cri
Kwanan baya, a nan birnin Beijing, 'yar wasan Piano Li Ang ta shirya wani taron nuna wasannin kide-kiden da ita kanta ta kada ta hanyar yin amfani da Piano a karo na farko a kasar Sin . Tun da take da shekaru fiye da goma, sai ta soma koyon ilmin wake-wake da kide-kide da nuna wasanni a kasashen waje, bayan da ta kware wajen nuna wasannin wake-wake da kide-kide na kasashen yamma, sai ta soma nuna wasannin wake-wake da kide-kide na kasar Sin ga masu sauraro na kasashen yamma. Yau za mu gabatar da wasu abubuwa dangane da yadda 'yar wasan Piano Li Ang ta yi karatu da samun kwarewa.

Wani 'dan kallon ya bayyana cewa, na ji ta yi kyau sosai , tana kwarewa sosai wajen kada Piano tare da nuna halinta mai kirki, amma ga alama ba ta nuna iyakacin kokarinta na faranta rai sosai wajen nuna wasan , amma daga duk fannoni ana iya ganin cewa, abin da ta yi na da kyau sosai wajen kada Piano.

Mahaifin Malama Li Ang shi ne wani injiniya , mahaifiyarta ita ce likita, dukansu suna kishin rera ko saurarar wake-wake da kide-kide. Malama Li Ang ta bayyana cewa, tun lokacin da take karama, tana more zaman rayuwarta cikin muryar wake-wake da kide-kide a gidansu, ta ce, tun lokacin da ta cika shekara daya, sai ta yi wasa da Piano, kullum mahaifinta da mahaifiyarta suna rera wakoki tare, ita kanta ta yi wasa da Piano, ya zuwa shekaru hudu da haihuwarta, ta soma koyon ilmin kada Piano, mahaifinta da mahaifiyarta dukansu sun nuna mata goyon baya wajen koyon ilmin wake-wake da kide-kide.

Da farko, Malama Li Ang ta soma karatu daga wasu abubuwan tushe na kada Piano, mahaifiyarta ta zabi wasu kide-kide masu saukin kadawa gare ta don kada ta rasa sha'awar kada Piano, a lokacin da ta cika shekaru 6 da haihuwa, karo na farko ne ta hau dakalin nuna wasanni, sai mahaifinta da mahaifiyarta sun soma amincewa da cewa, Li Ang tana da hazikanci sosai wajen kada Piano, sai suka kara karfinsu ga horar da ita wajen kada Piano, bayan da ta shiga makarantar firamare, sai ta kada Piano a kowace rana a lokacin hutu, ta hakan, ta kafa tushenta sosai wajen kada Piano.

A lokacin da malama Li Ang ta cika shekaru 10 da haihuwa, iyayenta sun tsai da kudurin aika ta zuwa kasar Amurka don ci gaba da koyon ilmin wake-wake da kide-kide.

A farkon da ta sauka kasar Amurka, ta sha wahaloli da yawa, ban da harshen Ingilish da ba ta kware ba, har ma ba ta saba al'adar da ake bi a kasar Amurka, sa'anan kuma hanyoyin da ake bi a kasar Amurka wajen koyar da ilmi na da bambanci da na kasar Sin, amma ba ta ji tsoron wadannan wahaloli ba, ta bayyana cewa, na sha wahaloli da yawa wajen koyon ilmin wake-wake da kide-kide a kasashen waje, amma wannan na da daraja sosai gare ni, duk saboda ina da sha'awar kada Piano, kuma a cikin zaman rayuwata, ba zan iya rashin kokarin kada Piano ba. A gaskiya dai ba abin sauki ba ne gare ni wajen kada Piano, amma dole ne na yi hakuri da shi. Ina kada Piano a kowace rana, in ba hakan ba, to ban ji dadi.

A lokacin da ta cika shekaru 13 da haihuwa, ta nuna wasanni tare da wasu manyan malaman kada Piano cikin hadin guiwa a cibiyar fasahohi na Linken da ke birnin New York, saboda haka Li Ang ta sami ci gaba sosai wajen kada Piano, kuma ta sami damar nuna wasannin sau da yawa , tana kara kwarewa, daga nan sai ta tsai da kuduri cewa, ba za ta raba da ita da wasan kada Piano, wato tana son kada Piano a duk zaman rayuwarta. (Halima)