Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-19 21:28:01    
Tattaunawar dake tsakanin shugabannin kasashen Sin da Cuba

cri

A ran 18 ga wata a bisa agogon wurin, a birnin Habana, shugaban kasar Sin Hu Jintao dake yin ziyara a kasar Cuba ya tattauna da Raul Castro Ruz, shugaban kwamitin gudanarwar kasar Cuba kuma shugaban taron ministocin kasar.

Inda shugaba Hu ya bayyana cewa, kasar Cuba kasa ce ta farko a cikin kasashen nahiyar kudancin Amirka wadanda suka kafa dangantakar jakadanci tare da kasar Sin. Halin da kasashen duniya ke ciki yanzu yana bukatar kasashen Sin da Cuba su ci gaba da bunkasa ayyukan hadin kai da sada zumunci a cikin tsawon lokaci mai zuwa, kuma wannan shi ne fatan jam'iyyun kasashen biyu da na jama'arsu.

Bugu da kari, shugaba Hu ya ba da shawarwari hudu a kan bunkasa huldar dake tsakanin kasashen biyu: ci gaba da ayyukan mu'ammala tsakanin manyan shugabannin kasashen biyu da zurfafa dangantakar siyasa a tsakaninsu, da kara mu'ammala mai sada zumunta tsakanin kasashen biyu, jam'iyyunsu, majalisun wakilan jama'ar kasashensu da gwamnatocinsu na matakai daban daban; zurfafa hadin gwiwa wajen tattalin arziki da ciniki da neman sabbin hanyoyi da fannonin hadin kai, don ciyar da aikin hadin gwiwa na tattalin arziki da ciniki dake tsakaninsu gaba; bunkasa mu'ammala mai sada zumunta da kara mu'ammala a fannin al'adun dake dacewa da 'yan adam, da kara mu'ammala da hadin kai a fannonin al'adu, ba da ilimi, kiwon lafiya da dai sauransu; karfafa hadin gwiwa a cikin batutuwan dake tsakanin bangarori da yawa, don kiyaye ikon kasashe matasa yadda ya kamata.

Shugaba Raul Castro Ruz ya yarda da kimantawar da shugaba Hu ya yi a kan huldar dake tsakanin kasashen biyu, kuma ya amince da shawarwarin da shugaba Hu ya bayar wajen bunkasa dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu. Kasar Cuba tana fatan bangarorin biyu za su ci gaba da zurfafa hadin kai a fannoni daban daban da kara fahimta da zumunta tsakanin jama'arsu. (Asabe)