Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-24 18:25:25    
Gwamnatin Sin ta kara mara wa masana'antu matsakaita da kanana baya ta fuskar kudi

cri
Tun daga farkon wannan shekara da muke ciki, kasar Sin ta kaddamar da tsuke bakin aljihunta domin hana raguwar darajar kudi. Amma a sakamakon sauye-sauyen halin da ake ciki a gida da kuma a waje a fannin tattalin arziki, kasar Sin ta fara sassauta kayyadewa kan bakin aljihunta sannu a hankali. A watan Nuwamba na wannan shekara, kasar Sin ta soke kayyadewar da aka yi a fannin ba da rancen kudi daga dukkan fannoni, ta kuma goyi bayan bankuna da hukumomin kudi da su kara mara wa masana'antu matsakaita da kanana baya a fannin ba da rancen kudi.

Yi Gang, mataimakin shugaban bankin jama'ar kasar Sin ya yi karin bayani cewa, wadannan manufofi sun nuna cewa, babban bankin kasar Sin yana nufin taimakawa masana'antu matsakaita da kanana wajen daidaita matsalar tattara kudade. Mr. Yi ya ce,"Tun daga watan Janairu zuwa watan Oktoba na wannan shekara, yawan karin rancen kudi da hukumomin kudi na kasar Sin suka bayar a fannoni daban daban ya kai kudin Sin yuan biliyan dubu 3 da dari 6 da 60, wanda ya kai matsayin koli a tarihi. Babu shakka irin wannan karuwa ta sanya dimbin masana'antu matsakaita da kanana su sami goyon baya ta fuskar rancen kudi."

A sa' i daya kuma, hukumomin kudi na kasar Sin sun kara sabunta hidimomin kudi, suna neman raya hanyoyin tattara kudade da masana'antu matsakaita da kanana za su bi. Alal musali, a birnin Dongguan na lardin Guangdong da ke kudancin kasar Sin, inda aka fi samun kanana da matsakaitan masana'antu, hukumar wurin da kamfanonin inshora da suka kafu domin manufofin kasar Sin sun samar da hanyar tattara kudade domin manufofin kasar, ta haka masana'antu matsakaita da kanana sun iya warware matsalar tattara kudade. Chen Qiwei, wani jami'in wurin ya yi karin bayani cewa, masana'antu matsakaita da kanana suna bukatar sayen inshora daga wadannan kamfanonin inshora kawai, sai sun iya samun hidimomin kudi ta fuskar saye-saye da tattara kudade daga wajen hukumomin kudi. Mr. Chen ya ce,"Idan ba a iya biyan bashi ba, sai hukumar kula da inshora da sayar da kayayyaki zuwa ketare za ta biya bashin da yawansa ya kai kashi 90 cikin dari, ta haka bankuna ba za su fuskanci babbar barazana ba."

Dadin dadawa kuma, a sakamakon taimako daga hukumomin da abin ya shafa, wasu masana'antu matsakaita da kanana sun tattara kudade ta hanyar cinikin hannayen jari da bankuna suka sayar a tsakaninsu a cikin gajeren lokaci. Sa'an nan kuma, hukumomin da abin ya shafa sun kara nuna goyon baya ga bunkasuwar kasuwar lissafi, domin sa kaimi kan masana'antu matsakaita da kanana da su tattara kudade ta hanyar kasuwar lissafi. Mr. Yi ya nuna cewa,"Idan ka lura da adadin kudi na kasar Sin, sai za ka gano cewa, a kwanan baya, a fannin karuwar rancen kudi, an sami saurin karuwar tattara kudade ta hanyar kasuwar lissafi."

Wani jami'in babban bankin kasar Sin da abin ya shafa ya bayyana cewa, har kullum wuyar tattara kudade da kuma samun rancen kudi da masana'antu matsakaita da kanana suke fuskanta tana damun kasashen duniya, shi ya sa ake bukatar dogon lokaci wajen warware wannan matsala bisa kokarin da ake yi. Nan gaba, babban bankin kasar Sin zai ci gaba da yin amfani da aikin ba da rancen kudi yadda ya kamata, domin mara wa masana'antu matsakaita da kanana baya ta fuskar ba da rancen kudi. Wadannan matakai sun hada da gaggauta kyautata da raya tsarin ba da hidimar kudi ga masana'antu matsakaita da kanana, da kara raya bankuna a garuruwa da kauyuka da kananan kamfanonin ba da rancen kudi da hukumomin taimakawa juna ta fuskar kudi a kauyuka da sauran sabbin hukumomin kudi, da kara sa kaimi kan kirkire-kirkire a fannin kudi da karfafa gwiwar bankunan kasuwanci da su rayawa da sabunta hanyoyin tattara kudade da hidimomin ba da rancen kudi da suke bai wa masana'antu matsakaita da kanana.(Tasallah)