Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-21 16:38:10    
Kauye na farko na kabilar Korea ta kasar Sin wato kauyen Jar tuta

cri
A gundumar Antu ta lardin Jielin da ke arewa maso gabashin kasar Sin, da akwai wani kauye wanda ya shahara a can wurin wato kauye mai sunan Jar tuta, akan kira wannan kauye da sunan kauye na farko na kabilar Korea ta kasar Sin, dalilin da ya sa haka shi ne, sabo da yawan mutanen wannan kauye ya wuce 300, amma dukkansu 'yan kabilar Korea ne. To jama'a masu sauraro, cikin shirinmu na yau za mu ja ku zuwa wannan karamin kauye na kabilar Korea don jin yadda jama'a suke jin dadin zamansu a can.

An gina gidajen kauyen Jar tuta a gefuna 2 na wata babbar hanyar mota, a hannun hagu dukkansu na da jajayen rufi ne da fararen bangwaye, a hannun dama kuwa suna da bakaken rufi ne da fararen bangwaye, amma dukkansu suna cikin inuwar itatuwa masu tsanwa shar da furanni masu launuka daban-daban. Mr. Li Zhuhao?ma'aikacin kwamitin kauyen wanda ya zo nan tun lokacin da yake da shekaru 9 da haihuwa, yanzu ya riga ya shafe shekaru fiye da 30 yana zaune a wannan kauye, ya gaya wa wakilinmu cewa,

"Na zo nan ne tun lokacin da nake da shekaru 9 da haihuwa, a lokacin can kuwa gidajen da aka gina a wannan wuri dukkansu bukkoki ne, hanyoyin da aka shimfida kuma dukkansu na tabo ne, ba a iya tafiya da sauki, idan an yi ruwa, dole ne a sa takalman ruwa."

An kasance haka tsawon shekara da shekaru, daga karshen gomiya ta 8 ta karnin da ya wuce kasar Sin ta fara tafiyar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, manufar nan kuma ta jawo tasiri ga wannan karamin kauye kan tudu, mutanen kauyen sun yi mamaki kuma suna zuba ido kan sauye-sauyen da ake yi a sauran wurare, su ma suna son zama masu arziki da wadata ta hanyar samun bunkasuwa da kansu. Mr. Li ya ce,

"Mun fara tafiyar da harkokin yawon shakatawa daga shekarar 1985, a shekarar 1989 kuma gundumarmu ta ba mu kudin taimako da yawa, lardinmu shi ma ya yi haka a shekarar 2004, sabo da haka mun samu karuwa sosai wajen sana'ar yawon shakatawa. A da, yawan kudin shiga da kowanenmu ke samu ya kai kudin Sin Yuan 3,000 kawai a shekara, amma zuwa shekarar bara yawan adadin nan ya karu har ya wuce Yuan 5,000."

Kauyen Jar tuta yana ta kara zaman wadata, mutanen kauyen kuma suna ta kara murna da farin ciki a kowace rana. Ban da wannan kuma suna kara mai da hankali domin kyautata zamansu na yau da kullum, sun yi sha'awar dasa itatuwa da furanni a kauyensu. Mr. Li ya ce,

"Yawan nau'o'in itatuwan da muka dasa ya wuce 20, ciki har da itatuwan pine da willow da dorowa, kowane iyali yana da nasa lambun furanni, kuma dukkansu sun dasa itatuwa masu ba da 'ya'ya, ka ga itatuwan parasol irin na kasar Sin da muka dasa suna da kyaun gani sosai."

Da akwai karin magana na cewar, "Idan an dasa itatuwan parasol irin na kasar Sin, za a iya jawo tsuntsayen phoenix wato fiffikau", irin wadannan fiffikau ba tsuntsaye ba ne, amma su ne mutane masu yawon shakatawa wadanda suka zo daga wurare daban-daban. Sun zo nan kauyen Jar tuta domin bude ido kan abubuwan al'adu da ake da su, a nan ne suke yin wasan lilo da sauran wasanni masu halayen musamman na kabilar Korea, kuma da hannunsu na kansu ne suke yin abincin gargajiya na kabilar Korea kuma suke dandana irin wannan abinci. Bayan cin abincin kuma, mutane abokai maza da mata, tsofaffi da yara na kauyen Jar tuta suna yin rawa da waka tare da su.

A ranar da wakilinmu ya je wurin domin samun labari, ya ga madam Jin Shunzi wadda take zaune a kauyen wadda kuma take sanye da tufafin gargajiya masu kyaun gani na kabilar Korea tana yawo a kan karamar hanyar kauye, cikin farin ciki ta rera wata wakar gargajiya ta kabilar mai sunan "Lemon zaki".

Jama'a masu sauraro, wannan ya bayyana cewa, mutanen da ke zaune a wannan karamin kauye na kabilar Korea suna zaune cikin hali mai sauki amma da farin ciki, to daidai sabili da wannan halayen musamman na jama'a ne, ake ta jawo mutane masu yawon shakawa wadanda da suka zo daga wurare daban-daban na kasar Sin da na kasashen waje.