Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-19 18:03:54    
Samun kiba fiye da kima ga matan da suka daina haila zai kara hadarin kamuwa da ciwon sankarar mama

cri
wani sabon nazarin da masu ilmin kimiyya da fasaha na kasar Amurka suka yi ya bayyana cewa, idan mata sun samun kiba fiye da kima bayan da suka daina haila, to sun fi saukin kamu da ciwon sankarar mama. Kuma idan nauyin jikinsu ya kara karuwa, to za a kara hadarin mutuwa sakamakon ciwon sankarar mama.

Kafin wannan, wani nazari ya taba bayyana cewa, ciwon da ka kamu da shi sakamakon samun kiba fiye da kima yana da nasaba da ciwon sankarar mama. Wannan nazarin da Maria Gammon na jami'ar North Carolina ta kasar Amurka ta yi ya tabbatar da irin wannan dangantakar da ke tsakanin cuttuttukan biyu. A 'yan kwanakin nan da suka gabata, ta ba da rahoto a gun taron shekara-shekara na kungiyar nazarin cuttuttuka da aka kamu da su sakamakon samun kiba fiye da kima ta Amurka da aka yi a birnin Boston, cewa a cikin matan da suka daina haila, yiyuwar kamu da ciwon sankarar mama ga wadanda suka samu kiba fiye da kima ya karu da kashi 75 cikin dari idan an kwatanta ita da wadanda suke da jiki sosai.

Ban da wannan kuma Madam Gammon ta bayyana cewa, dole ne mata su gane cewa, idan ki kamu da ciwon sankarar mama, kuma nauyin jikinki ya ci gaba da karuwa bayan da shekarunki ya kai 50 da haihuwa, to za ki fi saukin mutuwa.

To, masu sauraro, yanzu sai ku shakata kadan, daga baya kuma za mu yi muku wani bayani daban kan ciwon sankarar mama.

Wani sabon nazarin da masu ilmin kimiyya da fasaha na kasashen Turai suka yi ya bayyana cewa, game da mata masu kamu da ciwon sankarar mama wadanda aka yi musu tiyata don kare mamansu, yin musu jiyya ta hanyar yin amfani da haske mai karfi zai ba da taimako wajen shawo kan sake aukuwar ciwon.

Bisa labarin da aka samu daga tashar Internet ta watsa labarai kan ilmin kimiyya da ake kiranta "? Galileo" da ke karkashin jagorancin kungiyar sa kaimi ga samun ilmin kimiyya ta kasar Birtaniya, an ce, bayan da masu ilmin kimiyya na kungiyar hadin gwiwa don yin nazari kan sankarar mama ta Turai suka yi nazari, sun nuna cewa, ko shekarun da masu fama da sankarar mama ya yi yawa da haihuwa, ko suka taba samun jiyya, za a iya rage hadarin sake kamuwa da sankarar mama sosai gare su in suka samu jiyya ta hanyar yin amfani da haske mai karfi bayan da aka yi musu tiyata don kare mamansu.

Masu ilmin kimiyya da fasaha sun raba mata 7300 da aka yi musu tiyata don kare mamansu cikin kungiyoyi biyu ba tare da aka yi zabi ba, kuma an yi jiyya ga matan da ke cikin wata kungiya ta hanyar yin amfani da haske mai karfi, amma ba a yi haka ba ga matan da ke cikin kungiya dayan. Sakamakon nazarin ya bayyana cewa, idan ba mata wadanda kwayar sankara ta ratsa karinsu ba su karbi dabarar yin musu jiyya ta hanyar yin amfani da haske mai karfi ba, to kashi 46.5 bisa dari daga cikinsu ciwon sankarar mama da suka kamu da shi zai sake aukuwa. Amma jimlar ta kai kashi 13 bisa dari kawai ga wadanda suka karbar yin musu jiyya ta hanyar yin amfani da haske mai karfi.

To, jama'a masu sauraro, shirinmu na yau na ilmin zaman rayuwa ke nan. Muna fatan kun ji dadinsa, da haka Kande ta shirya muku wannan shiri kuma ke cewa a kasance lafiya.(Kande Gao)