Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-07 15:43:47    
Wurin yawon shakatawa na wasan Olympic a kan ruwa

cri

Wurin yawon shakatawa na wasan Olympic a kan ruwa, filin wasa kan ruwa ne na farko a tarihin wasannin Olympic, inda ake iya samun ruwa mai saurin gangara da kuma mai gangara sannu sannu a wani filin wasa daya. Ta haka za a yi gasannin tseren kwale-kwale da tseren kananan kwale-kwale da kuma wasan ninkaya a cikin wannan filin wasa. Bayan gasar wasannin Olympic ta Beijing, za a yi gasanni na gida da na duniya da kuma horar da 'yan wasa a nan, haka kuma fararen hula za su iya shiga wannan filin wasa domin motsa jiki ko kuma harkokin nishadi.

Fadin gine-ginen din din din a cikin wurin yawon shakatawa na wasan Olympic a kan ruwa ya kai misalin murabba'in mita dubu 18, sa'an nan kuma, fadin gine-ginen wucin gadi ya kai misalin murabba'in mita dubu 14. Fadin ruwan ya kai misalin murabba'in mita dubu 550. Bayan da aka cika hanyoyin gasa da ruwa, to, zurfin ruwan ya kai misalin mita 3.5, girman ruwan ya kai misalin cubic-metres miliyan 1 da dubu 700.

Babu tantama tilas ne a tabbatar da ingancin hanyoyin gasa, in aka haka irin hanyoyin gasa masu zurfi. Aiki mafi muhimmanci shi ne dole ne a aza harshi mai inganci, a hana ruwan ya shiga kasa. Kwararru sun sha yin dabara domin kammala wannan aiki.

Bayan da aka jarraba su ta hanyar cika su da ruwa, an sami kyakkyawan sakamako a fannin ingancin hanyoyin gasa. A watan Agusta na shekarar bara, an yi gasar fid da gwani ta tseren kwale-kwale ta matasa ta kasa da kasa a wurin yawon shakatawa na wasan Olympic a kan ruwa a Shunyi. Dukan bangarorin da abin ya shafa sun gamsu da wannan filin wasa sosai.


1 2