Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-06 12:51:02    
Kasar Afrika ta kudu ta nemi damar yin ciniki a kasar Sin

cri
Domin fuskantar da kalubalen da rikicin kudi da tabarbarewar tattalin arziki a duniya, 'yan kasuwa na kasar Afrika ta kudu suna kokarin kara yin hadin gwiwa da sabbin rukunnoni mafi saurin bunkasuwar tattalin arziki wadanda kasar Sin ke wakiltarsu a duniya don neman damar yin ciniki a kasar Sin, ta yadda tattalin arzikin kasar zai kubutar da mawuyacin hali.

An bude dandalin tattaunawa na tattalin arziki da ciniki da gwamnatocin birnin Shanghai da jihar Kwazulu Natal ta kasar Afrika ta kudu suka yi a ran 14 ga watan Oktoba a wani birnin dake kusa da bakin teku na gabashin kasar Afrika ta kudu. Inda ministan kudi da tattalin arziki na jigar Kwazulu Natal kuma shugaba mai jiran gado na jihar ya furta cewa, bunkasuwar tattalin arziki cikin sauri a kasar Sin ya kara damar yin ciniki tsakanin kasashen biyu. Kasashen Sin da Afrika ta kudu suna hadin gwiwa bisa tushen zaman daidai wa daida da kawo moriyar juna a fannoni da yawa, kuma fannonin da suke yin hadin gwiwa sun kara karuwa.

Ya kuma kara da cewa, bikin baje koli na kasar Afrika ta kudu da aka yi a ran 13 ga watan Oktoba a birnin Shanghai ya samu nasara sosai. Manyan kamfannoni 55 na kasar Afrika ta kudu sun shiga cikin wannan aiki tare, suna fatan za su shiga kasuwar kasar Sin a fannonin ma'adinai da fasahohin sadarwa da jiyya da halitta da fasahohin kiyaye muhalli da masana'antu da gyara amfanin noma da kera motoci da fasahar haka ma'adinai da na'urar sararin samaniya da sarrafa hanyoyin jiragen kasa ta hanyar fasahar zamani da dai sauransu, a sa'I daya kuma, za su iya kara yin hadin gwiwa da kamfannonin kasar Sin da kuma jawo jarin kamfannonin kasar Sin zuwa kasar Afrika ta kudu.

Yanzu, kasar Afrika ta kudu ta zama abokiyar ciniki mafi girma ta kasar Sin a nahiyar Afrika, yawan kudin da suka samu wajen ciniki tsakaninsu ya wuce dalar Amurka biliyan 14. Kasar Sin ta kafa manyan kamfannoni fiye da 100 a kasar Afrika ta kudu, jimlar yawan kudin da suka zuba ta kai dalar Amurka biliyan 6, manyan sana'o'In da suka shafa sun hada da fasahar makamashi da kudi da haka ma'adinai da kera kayayyakin gida masu aiki da wutar lantarki da tufafi da kuma samar da abinci da dai sauransu.

Hadin gwiwar kasashen Sin da Afrika ta kudu ya samu bunkasuwa sosai a cikin shekaru 10 da suka wuce. An labarta cewa, gwamnatin kasar Afrika ta kudu da hukumar kula da aikin bikin baje koli na kayayyakin duniya na Shanghai sun riga sun sa hannu kan kwagilar shiga bikin baje koli na duniya da za a yi a shekarar 2010 a birnin Shanghai. Inda kasar Afrika ta kudu kasa ce dake da yankin yin nuni mafi girma a kasashen Afrika ta kudu. Wasu manyan kamfannonin kasar Afrika ta kudu za su halarci bikin don neman damar yin ciniki a kasar Sin.

Jakadan kasar Sin dake kasar Afrika ta kudu Zhong Jianhua ya ce, hadin gwiwar kasashen Sin da Afrika ta kudu a fannin tattalin arziki da ciniki yana da makoma mai kyau. A shekarun baya, cinikin kasashen biyu ya samu bunkasuwa cikin sauri, bangarorin biyu sun samu sabon sakamako a fannin zuba jari ga juna, kamfannonin kasar Sin da dama sun kafa sansanin kera kayayyaki a kasar Afrika ta kudu, yawan kayayyakin da suka kera a shekarar 2007 ya kai dalar Amurka fiye da biliyan 1, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen bunkasuwar tattalin arziki da samar da ayyukan yi a wurin.

Ministan ciniki da masana'antu na kasar Afrika ta kudu ya furta cewa, hadin gwiwar kasashen biyu na da makoma mai kyau a fannonin kimiyya da fasaha da ba da hidimar kudi da sadarwa da kuma tarbiyya, kasar Afrika ta kudu tana fatan za ta kara yawan fannonin yin hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki tare da kasar Sin. Kasar Afrika ta kudu ta tsara manufofi masu gatanci ga wasu kamfannonin kasar Sin, kuma kamfannonin kasar Sin da yawa sun riga sun samu sakamako mai kyau a kasar Afrika ta kudu.(Lami)