Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-04 15:48:06    
Ziyarar Aljannar da ke duniyarmu

cri

A ganin mazaunan wurin 'yan kabilar Tibet, wannan wuri waje ne mai tsarki, dukkan abubuwan da ke cikin kwarin Allah ne ya ba su. Wata budurwa mai suna Yinamanhong, 'yar kabilar Tibet ta ce:

"Mu mazauna wurin 'yan kabilar Tibet mun gaskata cewa, dukan aububuwa suna da rayuka, tsaunuka da bishiyoyi da kuma ruwa Allah ne ya ba mu. Tilas ne mutane su kiyaye su, a maimakon lalata su. Tsoffi sun gaya wa 'ya'yansu, kada su wanke tufafi a cikin kogi, ko kuma ajiye abubuwa masu kazanta a cikin kogi."

Har zuwa yanzu 'yan kabilar Tibet suna ci gaba da zamansu a cikin wannan kwari, suna maraba da baki da hannu biyu biyu.

Bayan kai ziyara a kwarin Jiuzhaigou, sai muka ci gaba da ziyararmu a aljannar da ke duniyarmu, mun je shiyyar wurare masu ni'ima ta Huanglong, wadda ke da nisan kilomita 130 a tsakaninta da kwarin Jiuzhaigou. A shekarar 1992, hukumar UNESCO ta tanadi shiyyar Huanglong cikin 'takardar sunayen wuraren tarihi na halitta na duniya' tare da kwarin Jiuzhaigou. Wannan shiyya ta yi suna ne a fannin ruwa.

Masu yawon shakatawa su kan jin dadin kallon ruwan da ke cikin kwarin daga kan tsaunuka. A cikin kwarin, akwai wani tudu mai launin rawaya-rawaya mai tsawon kilomita 4 ya yi kama da wani haliffar dragon iri na kasar Sin mai launi zinariya, wanda ya kwanta a tsakanin bishiyoyi da tsaunukan kankara mai taushi. A kan wannan rawayan tudu akwai kananan tabkuna fiye da 3,000, su kan yi walkiya sosai saboda hasken rana. Tabkin da ke wuri mafi tsayi shi ne tabki mai suna Wucaichi, ya hada da kananan tabkuna misalin 700, wadannan kananan tabkuna sun nuna launuka iri daban daban domin hasken rana, ma iya cewa, su ne ainihin kyan ganin shiyyar Huanglong.


1 2 3 4