Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-03 17:01:39    
Labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri
---- Yawan kudin da aka samu wajen cinikin da ake yi tsakanin jihar Guangxi da kungiyar ASEAN wato kawancen kasashen kudu maso gabashin Asiya ya wuce dala biliyan 2 a karo na farko. Wannan bayani ya fito ne daga hukumar kwastan ta birnin Nanning na jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai ikon tafiyar da harkokin kanta da ke kudu maso yammacin kasar Sin

An labarta cewa, cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, hadin gwiwar da aka yi tsakanin kasar Sin da kungiyar ASEAN wajen ciniki ta hanyar zuba jari ya samu bunkasawa da sauri, ana nan ana ciyar da aikin raya shiyyar yin ciniki maras shinge tsakanin kasar Sin da kungiyar ASEAN gaba lami lafiya, hadin gwiwar da ake yi tsakanin shiyya da shiyya shi ma ya yi ta samun ci gaba. A farkon rabin wannan shekara kawai, yawan kudin da aka samu wajen kayayyakin shigi da fici a tsakanin jihar Guangxi da sauran kasashe 6 wato Vietnam da Malaysia da Singapore da Indonesia da Philippines da Brunei ya riga ya kai dala biliyan 2 da miliyan 120. Daga cikin su, yawan cinikin da aka yi tsakanin jihar Guangxi da kasar Vietnam ya kai kashi 84 cikin 10 bisa duk cinikin da aka yi a tsakanin jihar Guangxi da kungiyar ASEAN.

---- Kwanan baya a birnin Huhhot, an bude gasar wasan Qigong wato wani irin wasan motsa jiki na jan dogon numfashi a karo na 2 na kasar Sin, da akwai kungiyoyin wakilai da suka zo daga larduna da jihohi masu ikon tafiyar da harkokin kansu da birane da ke karkashin gwamnatin tsakiya kai tsaye 29 sun shiga gasar.

Wannan gasar da aka yi tana daya daga cikin jerin bukukuwan wasan Qigong na "yin wasan motsa jiki na dukkan jama'a da shirya wasannin Olimpic tare", cibiyar kula da wasan Qigong ta babbar hukumar wasan motsa jiki ta kasar Sin, da hukumar wasan motsa jiki ta jihar Mongoliya ta gida mai ikon tafiyar da harkokin kanta, da gwamnatin jama'a ta birnin Huhhot su ne suka shirya wannan gasa tare. Kuma da akwai mutane kusan 500 ciki har da 'yan wasa da malaman koyarwa na wasa da alkalan wasa da suka halarci wannan gasa cikin kwanaki 3. 'yan wasan kuma za su halarci gasanni iri 4 na kungiya-kungiya ko na mutum daya-daya tilo.

An ce, wasan Qigong yana hade da al'adun gargajiya na kasar Sin, kuma yana dacewa da mutane masu sha'awar wasannin motsa jiki kuma wadanda suka sha banbam wajen yawan shekarunsu da haihuwa , bisa matsayinsa na wani wasan motsa jiki na jama'a, ya samu maraba daga wajen tarin jama'a masu son motsa jiki sosai.