Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-03 19:37:47    
'Yan kasuwa na kabilar Hui sun taru a birnin Yinchuan don yin shawarwari kan batun bunkasa sana'o'in musulmi

cri

Kwanan baya an rufe babban taron 'yan kasuwa na kabilar Hui da taron koli na farko na musulmi masu masana'antu na kasar Sin wadanda aka shafe kwanaki 3 ana yin su a birnin Yinchuan, hedkwatar jihar Ningxia mai cin gashin kanta ta kabilar Hui da ke arewa maso yammacin kasar. A gun taron, masu masana'antu da kwararru masu binciken al'adun kabilar Hui da masanan ilmi wadanda jimlarsu ta kai kusan 500 da suka zo daga kasashe Sin da Amurka da Kirghistan da sauran wasu kasashe sun tattauna al'adun kabilar Hui wajen yin kasuwanci, da hanyar hadin gwiwa da kuma bunkasa sana'o'in musulmi.

Yawan musulmin da ake da su yanzu ya kai wajen miliyan 1,300 a duk duniya, a kasar Sin kuma da akwai kananan kabilu 10 ciki har da kabilar Hui da ta Uighur da ta Kazak wadanda dukkan mutanensu suke bin addinin musulunci, jimlar mutanensu kuma ta wuce miliyan 20, wadanda suke barbazuwa a wurare daban-daban na kasar Sin, musamman ma a arewa maso yammacin kasar.

Lokacin da Mr. Yang Zhibo, mataimakin shugaban hadaddiyar kungiyar musulmi ta kasar Sin ya tabo magana kan ma'anar wannan taron koli ya ce,

"Ta wannan hanya ce wato ta hanyar yin wannan taro ne, kabilar Hui da musulmi za su iya daga matsayin zaman rayuwarsu wajen tattalin arziki, haka ma wajen al'adu, da bunkasa tattalin arziki mai sigar musamman na kananan kabilu."

Tun fil azal musulmi sun kware wajen yin kasuwanci. Cikin littafin "Alkur'ani" da na "Bible" da aka rubuta, an tsai da cikakkun dokokin da'a wajen yin kasuwanci, kuma an dora harkokin kasuwanci bisa imani. Yau da shekaru fiye da 1,300 ke nan da musulmi 'yan kabilar Hui suka fara tafiyar da harkokin kasuwanci a duniya, har ma suka taba zama masu jagoranci kan harkokin cinikin kasashen waje. Bisa matsayinsu na 'yan kasuwa wadanda suke fadi-tashi ga yin ciniki, musulmi masu masana'antu ciki har da 'yan kasuwa na kabilar Hui sun ba da babban taimako ga bunkasa zaman al'umma da al'adu da cinikin kasar Sin, da kuma raya yankunan da ke bakin iyakar kasar.


1 2