Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-29 09:16:33    
Sakamakon ban mamakin da Jesse Owens ya kago

cri

A shekarar 1936, an bude zama na 11 na gasar wasannin Olympic ta Berlin, kodayake a wancen lokaci 'yan Nazi sun raina 'yan wasa bakaken fata ainun, amma a gun gasar nan, babban sakamakon da 'dan wasa bakar fata daga kasar Amurka Jesse Owens ya samu ya kai bugu ga ra'ayin kabilanci na Adolf Hitler sosai da sosai, kuma an mayar da shi bakar walkiya.

A gun gasar wasannin Olympic ta Berlin, Jesse Owens ya samu lambobin zinariya hudu, wato shi ne 'dan wasan guje-guje da tsalle-tsalle wanda ya fi jawo hankulan mutanen duniya a tarihin gasar wasannin Olympic ta zamanin yanzu, an haife shi a wani iyalin manoman auduga mai talauci dake kudancin kasar Amurka.

Tun yana yaro karami, sai Owens ya nuna babbar kwarewa kan wasanni. A gun taron wasannin motsa jikin daliban duk kasar Amurka da aka shirya a shekarar 1935, Owens ya karya matsayin bajinta na duniya na wasannin guje-guje da tsalle-tsalle sau biyar a cikin mintoci 45, kuma ya rike matsayin koli na duniya na wasan dogon tsalle da shekaru 25, daga nan Owens ya yi suna sosai a duk fadin duniya. Kafin gasar wasannin Olympic ta Berlin, Owens ya kago matsayin bajinta na wasan gudu na maza na mita 100, shi ma ya rike matsayin fiye da shekaru 20.

A gun gasar wasannin Olympic ta Berlin, Owens ya samu lambobin zinariya hudu wato na wasan gudun maza na mita 100 da wasan gudun maza na mita 200 da wasan dogon tsalle na maza da wasan gudun ba da sanda tsakanin maza hudu na mita 400. Sakamakon da Owens ya samu ba ma kawai ya kai bugu ga ra'ayin kabilanci na Hitler ba, har ma ya sa kaimi ga dukkan jama'ar kasashen duniya masu kishin zaman lafiya.

Bayan da Owens ya samu lambar zinariya ta wasan dogon tsalle, Hitler ya yi fushi sosai, kuma ya tashi daga kujera ya bar filin wasannin motsa jiki domin gujewa musafaha da kuma bai wa Owens lambar yabo.

Game da wannan, kwamitin wasannin Olympic na duniya ya bayyana cewa, idan shugaban kasar Jamus Hitler ya nuna kabilanci ga 'yan wasa, to, zai soke bikin bayar da lambobin yabo a gun wannan gasar wasannin Olympic. Amma Owens ya ce, ba damuwa, makasudin zuwansa a Berlin shi ne domin neman samun lambobin zinariya, ba domin yin musafaha ba.

A shekarar 1980, Owens ya riga mu gidan gaskiya, kuma an zabe shi 'dan wasa mafi gawurtacce na karni na 20. Don tunawa da sakamakonsa, an kafa lambar yabo ta Jesse Owens domin yaba wa 'yan wasa wadanda suka samu sakamako mai kyau na kasar Amurka. (Jamila zhou)