Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-27 21:13:31    
Mr. Wang Feihong, saurayi mai yin wasan karate na kabilar Miao ta kasar Sin

cri

Fannin al'adun kabilar Miao yana da fiffiko sosai daga cikin al'adun kananan kabilu da yawa na kasar Sin, musamma ma wasan karate na kabilar Miao ya taba zama abin koyi kuma ya samu karbuwa sosai daga waje mutane masu yin wasan karate na kasar Sin da na kasashen waje. To, jama'a masu sauraro, cikin shirinmu na yau za mu kai ku ziyara wajen Mr. Wang Feihong, mutum mai ba da misali wajen wasan karaten gargajiya na kabilar Miao.

Abin da kuke saurara shirin talebijin ne da aka watsa daga filin raba lambobin yabo a gun gasar tace gwanayen wasan karate da Mr. Wang Feihong ya halarta a koro na farko. To daidai sabili da wannan gasa ce, Mr. Wang ya zama dan wasan karate tamkar wani tauraro mai haske wanda kowa ya san shi a kasar Sin.

A shekarar 2006, Mr. Wang Feihong ya yi rajistar shiga gasar wasan karate da wani gidan talebijin kasar Sin ya shirya, a gun gasar ya nuna wasan da shi kansa ya shirya, kuma ya zama zakara.

Mr. Wang Feihong an haife shi ne a shiyyar tudu mai nisa da ke yankin kabilar Miao da ta Dong mai ikon tafiyar da harkokin kansa na lardin Guizhou da ke kudu maso yammacin kasar Sin, yawancin mutane da ke zama a can su ne 'yan kabilar Miao da ta Dong da sauran kananan kabilu. Tun lokacin da yake da shekaru 7 da haihuwa, ya fara nuna sha'awa ga wasan karate, kuma ya fara koyon wasan kung-fu na gargajiya na kabilar Miao. Lokacin da yake da shekaru 15 zuwa 16 da haihuwa, ya fara kollon sinima da Bruce Lee ya nuna, sabo da haka ya kara nuna sha'awa sosai ga wasan karate, kuma ya yi wasan karate ta hanyar hada wasan kung-fu na gargajiya na kabilar Miao da irin wasan karate da Bruce Lee ya kirkiro.

Daga baya, Mr Wang Feihong ya ci jarrabawar shiga cikin kungiyar masu waka da rawa ta kabilu ta wurin da yake zama sakamakon gwanintar da ya nuna wajen wasan karate. Cikin kungiyar ba ma kawai ya yi wasan karate ba, kuma ya yi koyi da fasahar rera wakoki da yin raye-raye da fasahar yin kide-kiden gargajiya.

Amma, yin waka da rawa ba burin Mr. Wang ba ne, shi ya sa bayan da ya shafe shekara daya da rabi yana aiki cikin kungiyar masu waka da rawa, sai ya zo nan birnin Beijing shi kadai. Domin tabbatar da burinsa, yakan tashi daga barci wajen karfe 6 na kowace rana da safe domin yin wasan karate, kuma yana aiki ba dare ba rana domin ciyar da kansa. Ya ce, "Kome aiki da na yi dukkansu domin cimma burina ne, burina kuwa shi ne da farko ciyar da kaina, daga baya kuma zan tabbatar da mafarkina. A farkon lokacin zuwana nan birnin Beijing, na taba gamuwa da wahaloli da yawa sabo da ba ni da abokai, amma na amince cewa idan na koyi abubuwa da yawa, kuma idan da dama, zan iya nuna kwarewata."

A shekarar 2006, Mr. Wang Feihong ya tsai da kudurin shiga shirin zaben kwararrun wasan karate da gidan talebijin ya watsa, a gun gasar, ya sa tufafin da shi kansa ya tsara fasali, kuma ya nuna wasan da shi kansa ya shirya, a karshe kuwa ya samu nasara har ya zama zakara, sabo da haka kuma ya zama dan wasan karate wanda kowa ya san shi a kasar Sin, har ma mashahuran daraktocin kula da harkokin sinima na Hongkong sun sa ido kan sa, kuma ya sha zama muhimmin dan wasa cikin wasannin kwaikwayo na talabijin.

Cikin wasannin kwaikwayo da yawa na talabijin, Mr. Wang Feihong yakan zama dan wasa mai cike da kuzari wanda kuma ya ba 'yan kallo zurfaffiyar alama a zukatansu, amma a zaman yau da kullum, Mr. Wang wani mutum ne mai dattaku da saukin kai, ba kawai ya iya waka da rawa ba, hatta ma ya iya bushe-bushe da kade-kade. To jama masu sauraro, yanzu za mu sanya muku wata waka mai sunan "Mangdayo" wadda Mr. Wang ya rera, Yanzu Mr. Wang ya riga ya cim ma burinsa, amma yana ganin cewa, wannan ya zama masomi ne wajen tabbatar da mafarkinsa, yana son yin farfagandar wasan kung-fu na kabilar Miao zuwa duk duniya baki daya.