Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-23 15:12:42    
Mutanen Baotou na jihar Mongoliya ta gida sun yi iyakacin kokarinsu wajen kare wurare masu damshi

cri

A cikin shirinmu na yau za mu gabatar muku da wani bayani kan yadda mutanen Baotou suke yin iyakacin kokarinsu wajen kare wurare masu damshi. Rawayar kogi da ta ratsa jihar Mongoliya ta gida mai ikon tafiyar da harkokin kanta dake arewancin kasar Sin d wurare masu damshi dab da kogi sun taka muhimmiyar rawa wajen kare kwararowar hamada kuma su ne albakartan hallita marasa na biyu a kasar Sin kasancewar kogin da wurare masu damshi ta ba da muhimmin taimako wajen daidaita yanayin birnin Baotou,birni mafi girma na masana'antu a jihar Mongoliya ta gida,haka kuma ta tsabta iskar dake cikin birnin.Domin kiyaye wurare masu damshi daga dukkan fannoni,gwamnatin birnin Baotou ta tsaida kudurin zubar kudin Sin Yuan miliyan daya domin tabbatar da shirin kiyaye wurare masu damshi. Da zarar a kammala shirin madatsar ruwan kogin za ta kara inganta da wurare masu damshi na kara kyautatuwa.

A kasar Sin an ce wurare masu damshi su ne kodar duniya.idan kana zama cikin biranen dake da wurare masu damshi,za ka iya cin moriyar da wurare masu damshi suka kawo maka.wurare masu damshi ba ma kawai suna iya samar da abinci da abubuwa masu amfani da ruwa ga dan Adam ba,hatta ma sun taka rawar gani wajen kiyaye muhalli da kasancewa abubuwa masu rai barkatai da tanadin ruwa da magance ambaliyar ruwa da fari da kuma daidaita yanayi.

Bisa kididdigar da aka yi,an ce da akwai wurare masu damshi na kadada sama da dubu 36 a yankin da birnin Baotou ke mallaka a jihar Mongoliya ta gida mai ikon tafiyar da harkokin kanta a halin yanzu,daga cikinsu fili mai fadin kadada dubu talatin,wurare masu damshi ne na dab da rawayan kogi,suna cikin wani ziri mai tsawon kilomita 220 da ke cikin yankin birnin Baotou da rawayan kogin ta ratsa.Duk da haka wurare masu damshi da ke cikin yankin Baotou ba su cikin wani hali mai faranta rai ba a yanzu. Bisa labarin da aka samu,an ce wurare masu damshi da dama dab da rawayan kogin an yi amfani da su wajen yin tubali ko kiwon kifaye ko gina dakunan cin abinci. Domin kiyaye wurare masu damshi ta yadda su zama kariya ga biranen dab da rawayan kogin, a watan Maris na shekarar 2008 gwamnatin jama'a ta birnin Baotou ta tsaida kudurin tsabtace da inganta wurare masu damshi dab da rawayan kogin. Tun daga ran 1 ga watan Afrila na wannan shekarar da muke ciki ma'aikata na sassan da abin ya shafa na birnin Baotou sun fara rushe wuraren yin tubali da na kiwon kifaye da kawa da gine ginen da aka kafa ba bisa doka ba.


1 2 3 4 5