Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-22 15:18:14    
Gasar wasannin Olimpic ta kori yaki

cri

Jama'a, yanzu ga shirinmu na sharhin da shahararrun mutanen duniya suka yi kan wasannin Olimpic. Yau za mu gabatar muku da wani bayanin da ke da lakabi haka: Gasar wasannin Olimpic ta kori yaki.

A lokacin da ake shirya gasar wasannin Olimpic ta Bejing, ana ta saurarar amon bindiga maras jituwa a shiyyar Ossetia ta kudu ta kasar Georgia, wannan sosai da sosai ya bayyana dawainiya mai muhimmanci ta wasannin Olimpic ta shimfida zaman lafiya da mawuyacin halin da ake ciki don aiwatar da dawainiyar. Kwanan baya, wakilin gidan rediyon kasar Sin ya ziyarci wasu 'yan wasa da masu koyarwa da jami'ai na kasashen waje da ke halartar wasannin Olimpic na Beijing , inda gaba daya ne suka bayyana burinsu na gaba daya, wato yin adawa da yaki da kuma yin addu'a domin zaman lafiya, yanzu za mu bayyana wani bayanin da wakilin gidan rediyon kasar Sin ya ruwaito mana, sunan bayanin shi ne, gasar wasannin Olimpic ta kori yaki.

Wasannin Olimpic ba ma kawai shi ne kasaitaccen taron wasannin motsa jiki da aka yi bisa babban mataki a duniya ba, hatta ma wani taron ganawar juna na sada zumunta a tsakanin jama'a masu kishin zaman lafiya na duk duniya. Kafin babban yakin duniya na farko, bisa halin dakatar da yaki cikin tsarki na wasannin Olimpic na zamani aru aru , Pierre de Coubertin, mutumin farko da ya soma shirya wasannin Olimpic na zamanin yau ya bayyana burin nan na dakatar da yaki a lokacin gudanar da wasannin Olimpic. A shekarar 1993, gaba daya ne babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya zartas da kudurin dakatar da yaki a lokacin gudanar da wasannin Olimpic. Saboda haka, tunanin zaman lafiya na wasannin Olimpic yana kara shiga zuciyar mutane a kowace rana.

'Dan wasan ninkaya da ke da shekaru 19 da haihuwa mai suna Ahmed Adam ya zo nan daga kasar Sudan. Ya bayyana cewa, lokacin yakin basasa da aka yi a kasar Sudan ya kai rabin karni, jama'ar Sudan suna shan wahalhalun yaki mai tsanani sosai , saboda haka, 'yan wasan kasar Sudan suna fahimtar tunanin zaman lafiya da wasannin Olimpic ya gabatar sosai da sosai, ya bayyana cewa, a lokacin gudanar da wasannin Olimpic, jama'ar kasashe daban daban ya kamata su kubutar da kansu daga matsaloli, kodayake kasashe daban daban na duniya suna wurare daban daban, amma tutarsu suna karkadawa a filayen gasar wasannin Olimpic, hanyar nan da aka bi a tarihi ta alamanta zaman lafiya, halin wasannin Olimpic ya yi kira ga shimfida jituwa da zaman lafiya da kuma yin shawarwari.

'yar wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta kasar Iraq mai suna Dana Abdel Razak ta bayyana cewa, a shekarar 2006, a cikin gidan kasar Iraq, an tayar da tsanantattun al'amura sau da yawa na kama mutane don yin garkuwa da kuma yi wa mutanen da ke cikin rukunonin wasan motsa jiki kisan gilla, ita da kanta ta kuma gamu da hare-hare sau da yawa da aka yi mata. Tun daga farkon shekarar da muke ciki har zuwa yanzu, kodayake halin da ake ciki a kasar Iraq ya sami 'yar kyautatuwa, amma ba a iya sa ran faranta rai ba. Ta ce, ba ni kadai kawai da na sami irin wannan al'amari, wato harin ta'addanci ba, na tabbatar da cewa, kowanen mutumin da ya ke zama a kasar Iraq, mai yiyuwa ne zai gamu da irin wannan al'amari, duk saboda muke zama a karkashin halin yaki. Jami'in watsa labaru na ofishin jakadancin kasar Iraq da ke kasar Sin wanda ya rufa wa Dana Abdel Razak baya a wannan gami ya bayyana cewa, wasan motsa jiki na da karfin halittu na hada kan jama'a da yin adawa da yaki, ya bayyana cewa, makasudin kai hari ga 'yan wasa da masu tsatsauran ra'ayi suka yi shi ne don hana su shiga gasannin da ake yi a kasa da kasa, kuma sun yi hakilon banza na yanke cudanyar da ke tsakanin kasar Iraq da kasashen waje. Ya ce, 'yan wasan motsa jiki suna iya nuna alamomi masu muhimmanci sosai, suna iya haduwar jama'ar kasar Iraq da ke da ra'ayoyi daban daban gu daya, saboda haka, sun zama takitin farko da masu kai hari suka kai musu hari . Amma, kokarin da 'yan wasan motsa jiki suke yi ba tare da kasala ba da tsayayyar niyyarsu suna sanya wa duk kasar Iraq su kara musu himma. A wannan karon da suke zuwa nan don shiga gasar wasannin Olimpic, muna jin farin ciki da alfahari sosai da sosai .

Mai koyarwar wasan guje-guje da tsalle-tsalle mai suna Youssef Hamadna da ya zo daga Palesdinu ya bayyana cewa, hargitsin da ake yi tsakanin Palesdinu da Isra'ila har cikin rabin karni ko fiye ya riga ya sa bangarorin biyu wato Palesdinu da Isra'ila da sauran jama'ar kasashen da ke shiyyar sun ci hasara mai tsanani. Ya bayyana cewa, bayan da 'yan wasan motsa jiki na Palesdinu su da kansu su sa ido kan kwanciyar hankali da wadatuwa da kasar Sin ta samu, sun burge sosai, suna bege cewa, kasarsu za su iya samun zaman lafiya tun da wuri, ya ce, na yi mafarki da cewa, idan muhallin horar da mu da sharadin horar da mu na da kyau, mai yiyuwa ne za mu koma tare da murmushi ga yara da jama'a na Palesdinu, shiga cikin gasar wasannin Olimpic kawai bai isa ba , ya kamata mu sami wasu sakamako, sakamakon ba alamomin yabo kawai ba, amma ya kamata a sami sakamako mai kyau, kuma ta hanyar, za a bayyana wa jama'ar kasashe daban daban cewa, mu ne kabila mai wayewar kai, amma ba kabilar nuna ta'addanci ba, muna son shimfida zaman lafiya tare da jama'ar kasashe daban daban, musamman ma shimfida zaman lafiya mai gaskiya tare da jama'ar Isra'ila.

Tun daga shekarar 1979 har zuwa yanzu, wutar yakin da aka yi cikin shekaru kusan 30 ya mayar da kasar Afhanistan don ta zama daya daga cikin kasashe mafi talauci da koma baya sosai a duniyar yau. Shugaban kungiyar wakilan wasan motsa jiki ta kasar Afhannistan da ke halartar wasannin Olimpic na Beijing Mr Sayed Mahmood Zia Dashti ya bayyana cewa, wasannin Olimpic ya gabatar da sabuwar dama ga kasar Afhannistan don jawo hankulan gamayyar kasa da kasa, ya ce, yakin ya sa duniya ta manta da Afhannistan a kwana a tashi, tsanataccen halin tsaro da ake ciki a 'yan shekarun nan da suka wuce ya yi ta kawo wa kasarmu ta mahaifa masifa mai tsanani sosai, wasannin Olimpic ne ya sa kasar Afhanintan da ta sake koma a karkashin idannun kasashe daban daban, ya kuma kara da cewa, wasannin Olimpic ma ya kawo wa samarin kasar Afhannistan sabon fata. Ya ce, ana iya tsammani cewa, ta hanyar kafofin watsa labaru daban daban, samarin kasar Iraq suna kallon abubuwan da 'yan wasan kasarsu suka yi a wasannin Olimpic, za su yi wa kasarsu ta mahaifa alfahari, za su kuma manta da wahalhalun da yaki ya kawo musu. Wasannin Olimpic ya kawo musu fata.(Halima)