Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-14 16:56:45    
Jihar Ningxia ta kasar Sin ta samu sakamako mai kyau wajen shawo kan kwararowar hamada

cri

Bisa kididdigar da aka bayar, an ce, kafin shekara ta 2000, yankunan jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kai ta kasar Sin da fadinsu ya kai kashi 65 cikin dari da kuma mutanen jihar da yawansu ya kai kashi 90 cikin dari sun samu barazana daga kwararowar hamada bisa matsayi daban daban, hamada mai tsanani ta yi mummunar illa ga ayyukan samarwa da zaman rayuwar jama'ar jihar. Gundumar Yanchi tana daya daga cikin yankunan jihar Ningxia da suka fi shan wahalar kwararowar hamada. Bisa binciken da aka gudanar a shekara ta 1983, fadin hamada ya kai fiye da kashi 40 cikin dari bisa dukkan fadin yankunan gundumar. Lokacin da aka tabo mumunan muhallin halittu na wancan lokaci, Zuo Wenzhu, wani dan kauyen Erbukeng na gundumar Yanchi ya bayyana cewa,

"Ko da na gaya maka, tabbas ne ba za ka ba da gaskiya ga halin da muka taba kasancewa ba, wato a lokacin da, in akwai iska, to hamada za ta kwarara kamar ruwa, ana iya samun hamada a ko ina a kasa. Haka kuma a lokacin da, ba a iya yin shuke-shuke ba, dalilin sa ya sa haka shi ne sabo da hatsi su kan mutu sakamakon iska ta kan kado rairayi a yanayin bazara. Ban da wannan kuma ba a iya dasa ciyayi ba, kuma ba a iya kiwon tumaki ba."

Domin kawar da illar da kwararowar hamada ta yi wa bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'ummar jihar Ningxia, bi da bi jihar ta dauki matakai daban daban wajen shawo kan kwararowar hamada. Alal misali, an daina karbar wasu haraji ga masana'antu da mutane da suka dasa bishiyoyi da ciyayi a sabuwar kasar da ba a taba noma ba, kuma an kebe dimbin kudade wajen raya kayayyakin ban ruwa iri daban daban, haka kuma an kaddamar da manyan ayyukan kiyaye muhallin halittu wajen hana kiwon dabbobi a kan duwatsu da mayar da gonaki don su zaman gandun daji da kuma ciyayi.


1 2