Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-10 18:09:13    
Kasar Sin ta samu bunkasuwar sha'anin ba da ilmi da sauri a cikin shekaru 30 da suka gabata

cri

Tun bayan shekarar 1978 har zuwa yanzu, kasar Sin ta samu babban sakamako daga sha'anin ba da ilmi, wato ta cim ma burinta cikin shekaru 30, amma kasashe masu sukuni sun cim ma burinsu cikin shekaru dari guda. A halin yanzu dai, kasar Sin ta riga ta cim ma burin ba da ilmin tilas na shekaru 9, da kuma yaki da jahilci ga matasa, haka kuma yawancin jama'a yanzu suna iya samun ilmi mai zurfi.

A cikin wani dogon lokacin da ya gabata, gwamnatin kasar Sin ta mai da hankali sosai kan sha'anin ba da ilmi. Musamman ma bayan da kasar Sin ta fara yin gyare gyare a gida da bude kofa ga duniya, gwamnatin kasar Sin ta kara zuba jari a kan sha'anin ba da ilmi, sakamakon haka ne, sha'anin ba da ilmi na kasar Sin ya samu bunkasuwa cikin sauri.


1 2 3 4