Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-10 15:30:20    
Jami'an tawagogin kasashe daban-daban na duniya sun buga babban take ga bikin bude gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing

cri

Aminai 'yan Afrika, kamar yadda kuka san cewa a yanzu haka dai, ana gudanar da gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing. Amma a cikin shirinmu na yau dai, bari in dan gutsura muku wani bayani kan wata 'yar wasan lankwashe jiki wato artistic gymnestics mai suna Wania Monteiro daga kasar Cape Verde. Bayanin na da lakabi kamar haka: " Na yi alfarmar halartar gasar wasannin Olympics ta Beijing a madadin kasar mahaifata".

Malama Wania Monteiro, wata karamar yarinya ce ramammiya wadda kuma ba ta da nakasa a jiki daga kasar Cape Verde. Gasar wasannin Olympics ta Beijing, gasar wasannin Olympics ce da ta halarta a karo na biyu. A gun gasar samun izinin shiga wasan lankwashe jiki mai fasaha a dukkan fannoni tsakanin mace dai-dai, yarinya Wania Monteiro ta sha kaye bayan ta zo ta 24 a gun gasar. Saboda haka ne, ba ta samu damar shiga gasar karshe ba. Amma duk da haka, ta yi farin ciki da fadin cewa, lallai ta yi nasara saboda ta samu damar shiga filayen wasannin Olympics a wannan gami bayan ta haye tulin wahalhalu. Kuma cewa ta yi, ta yi alfaharin halartar gasarwasannin Olympics ta Beijing a madadin kasar mahaifarta.

Malama Wania Monteiro mai shekaru 22 da haihuwa, wata daliba ce ta wata Jami'ar koyon ilmin talla ta kasar Brazil. Sanin kowa ne, ya kasance da nisa ainun tsakanin kasar Brazil da kasar Cape Verde. Domin samun karin ilmi a Jami'ar, Malama Wania ba ta da lokuta da yawa wajen share fagen halartar gasar wasannin Olympics ta Beijing. Amma duk da haka, ta nuna bajimta wajen yin horo da zummar nuna kwarewarta a gun wasannin Olympics na Beijing. Daga baya dai, Malama Wania ta fadi cewa, gine-ginen wasan motsa jiki da kasar Cape Verde take da su ba na abun a-zo-a-gani ba. Saboda haka, takan samun horo tare da 'yan wasa na sauran ayyukan wasa a wani filin horaswa daya. Tana mai cewa:" Ba mu da wurin musamman na yin horo a fannin wasan lankwashe jiki na fasaha. A galibi dai, mukan yi horo a dakin wasan kwallon kwando tun daga karfe 3 zuwa karfe 5 na yamma a kowace rana, domin bayan wannan lokaci 'yan wasan kwallon kwando, da kwallon tafin hannu da kuma na kwallon raga sukan yi horo a nan. Ban da wannan kuma, ba mu da madubi da akwatin watsa sautin kida. Amma duk daka, mun yi iyakacin kokari wajen yin horo".

Malama Wania Monteiro ta kara da cewa, ta soma koyon ilmin wasan lankwashe jiki na fasaha ne tun da ta samu shekaru 7 da haihuwa. Daga baya dai, ta nuna sha'awar wannan wasa kwarai da gaske! Wania ta shafe shekaru 15 tana zama tare da wasan lankwashe jiki na fasaha. Ko da yake ba ta samu maki mai kyau a wannan fanni ba, amma a ganinta, halartar gasar lankwashe jiki na fasaha a gun wasannin Olympics ya ba ta damar tabbatar da darajar da take da ita. Ta fada wa wakilinmu cewa:" Lallai ba kowane dan wasa da ya samu damar shiga gasar wasannin Olympics ba. A yau dai, na sake tsayawa kan filin wasanni na Olympics a madadin kasar mahaifata, inda na kara da 'yan wasa mafi kyau na duniya a wuri guda. Abun ya kasance wani gwaji ne mai daraja da na samu a duk tsawon rayuwata".

Malama Wania Monteiro ta furta cewa, gasar wasannin Olympics ta Beijing ta kasance ta karon karshe da ta halarci gasar wasannin Olympics. Muddin ta sauye karatu a Jami'ar din, za ta koma wa gida, inda za ta bude wani ofishin zayyana tallace-tallace na kanta. Ta ce, lallai abun ya dace in har ta zabi wannan lokaci don barin dandalin wasan lankwashe jiki na fasaha duk da bakin jiki da ta ji saboda rashin cigaban yin wannan wasa. Ta fadi cewa, za ta bi wani salo daban wajen cigaba da rayuwar wasan motsa jiki. Tana mai cewa: " Ko da yake zan yi aiki a fannin talla bayan sauye karatu a Jami'ar, amma duk da haka, ba za yi watsi da wasan lankwashe jiki na fasaha ba. Ina da shirin shiga kwas din horar da alkalai na wasan lankwashe jiki na fasaha da zummar ci gaba da bada taimako ga sha'anin wasan motsa jiki na kasar mahaifata".

Lallai Malama Wania Monteiro ba za ta manta da gajeren lokacin da ta yi zama a nan Beijing ba har abada, musamman ma rana ta biyu da aka bude gasar wasannin Olympics ta Beijing, wato rana ce ta cika shekaru 22 da aka haife ta. Wania ta ce tana mai kaunar wannan kyakkyawan birni, inda na samu ilmin al'adun kasar Sin. Ta yi farin ciki da fadin cewa: " Na samu karin ilmi game da kasar Sin yayin da nake neman fahimtar al'adun wanann kasa, wanda ya sha bamban ainun da namu. A ganina, irin wannan bambanci ba zai kawo cikas ga musanyar da muke yi tsakaninmu ba".

Ga Malama Wania kyakkyawa ta kawo karshen rangadinta a gun gasar wasannin Olympics ta Beijing, kuma za ta dasa aya ga rayuwar 'yar wasa, amma mun hakkake, za ta samu sabon cigaba a kan hanyar rayuwarta a nan gaba. ( Sani Wang )