Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-07 12:59:50    
Cibiyar wasanni ta wasan Olympic ta Beijing

cri

Masu karatu, yanzu bari mu ci gaba da ziyararmu a nan Beijing, hedkwatar kasar Sin, kuma za a yi gasar wasannin Olympic ta Beijing a wannan shekara. Za a yi wasu shirye-shirye na wasan pentathlon na zamani da shirin wasan kwallon hannu ta gasar wasannin Olympic ta Beijing ta shekarar 2008 a wannan filin wasa da zan gabatar muku da shi a wannan karo, wato cibiyar wasanni ta wasan Olympic ta Beijing.

An kafa cibiyar wasanni ta wasan Olympic ta Beijing a shekarar 1987. Wannan cibiya ta hada da wani filin wasa da kuma wani dakin wasa. A karshen watanni 6 na shekarar bara, an kammala yi mata kwaskwarima.

In an shiga cibiyar wasanni ta wasan Olympic ta Beijing daga kofarta ta gabas, da farko dai, za a ga dakin wasa na wannan cibiya. Za a yi shirin wasan kwallon hannu na gasar wasannin Olympic ta Beijing a wannan dakin wasa mai fadin misalin murabba'in mita dubu 30. A lokacin gasar wasannin Olympic ta Beijing, wannan dakin wasa zai karbi 'yan kallo fiye da dubu 5 da dari 7. Muhimmin bangare na wannan dakin wasa mai launin fari ne, an kuma yi masa bisa tsarin gine-gine na gargajiya na kasar Sin. Irin wannan tsantsar tsarin gine-gine na gargajiya na kasar Sin ya sanya wannan dakin wasa ya zama daya daga cikin alamun cibiyar wasanni ta wasan Olympic ta Beijing.

Kazalika kuma, a tsakiyar wannan cibiyar wasanni akwai wani filin wasa a waje. Za a yi sassan wasa da dawaki da na gudu na shirin wasan pentathlon na zamani na gasar wasannin Olympic ta Beijing a shekarar da muke ciki. A matsayinsa na wani babban filin wasa, an ajiye hanyoyin gudu na roba da hanyoyin tsarin sadarwa na zamani da babban allon nuna hotuna masu launuka da sauran na'urorin gasa na zamani ko kuma na aikin sadarwa na zamani. A shekarar 1989, hukumar Beijing ta gina wannan filin wasa ne domin shirya gasar wasanni ta Asiya a karo na 11. A lokacin, fadin filin wasan ya kai misalin murabba'in mita dubu 20, ya iya karbar 'yan kallo dubu 18. Domin shirya gasar wasannin Olympic ta shekarar 2008 a nan Beijing, hukumar Beijing ta fadada wannan filin wasa da ke cibiyar wasanni ta wasan Olympic ta Beijing. Bayan da aka fadada shi, jimlar fadin filin wasan ya kai misalin murabba'in mita dubu 37, yawan 'yan kallo da filin wasan ya iya karba ya kai dubu 40, wato ke nan irin wannan adadi ya ninka sau daya ko fiye. Baya ga fadada shi, an kuma ajiye dimbin na'urorin da aka samar da su bisa tunanin 'mayar da mutane a gaban kome' a cikin wannan filin wasa. An hada tsari mai aiki da kansa na yi wa wurin gasa ban ruwa na zamani da tsarin ba da gargadi kan aukuwar gobara da kuma tsarin sa ido domin tabbatar da tsaron lafiyar mutane. Sa'an nan kuma, an samar da karin yawan dakunan da abin ya shafa da kuma kananan dakuna.

Bayan da aka yi musu kwaskwarima, Beijing ta sami karin manyan filayen wasa 2 da suka tabbatar da ma'aunin shirya shirye-shiryen gasar wasannin Olympic, sa'an nan kuma, suke iya samun bakuncin tarurukan nune-nune da wasannin kwaikwayo.