Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-07 12:58:32    
Hukumar ilmi ta kasar Sin ta yi kokari wajen ba da tabbaci ga dalibai masu fama da girgizar kasa don shiga jarrabawar neman shiga jami'a

cri

Sabo da illar da mummunar girgizar kasa ta yi, dalibai dubu 120 na gundumomi 57 na lardunan Sichuan da Gansu na kasar Sin da suka fi fama da bala'in ba su iya shiga jarrabawar neman shiga jami'a tare da dalibai fiye da miliyan 10 na sauran birane da larduna a sa'i daya ba, wadda a kan yi a ran 7 da ran 8 ga wata. Bayan da gwamnatocin wurin suka yi nazari a tsanake, ma'aikatar ilmi ta kasar Sin ta amince da cewa, an jinkirta lokacin shiga jarrabawar neman shiga jami'a ga daliban da suka zo daga yankunan da suka fi fama da bala'in girgizar kasa domin tabbatar da lafiyarsu. Za a yi jarrabawar bayan wata guda, ta yadda daliban za su iya daidaita tunaninsu, kuma za a iya sake gina dakunan makarantu da wuraren yin jarrabawar.

Gundumar Wenchuan tana daya daga cikin yankunan lardin Sichuan da aka jinkirta lokacin jarrabawar neman shiga jami'a, inda wakilinmu ya gano cewa, an lalata dakunan wata makarantar sakandare sakamakon girgizar kasa, dalibai fiye da 800 da za su shiga jarrabawar sun mayar da tantunan da aka gina a filin wasanni a matsayin azuzuwan wucin gadi. Wani dan makaranta Tian Yangsong ya gaya wa wakilinmu cewa, gwamnatin wurin tana gina wasu dakunan tafi-da-gidanka nan kusa, za su iya sake samun darussa a can ba da jimawa ba. Kuma ya kara da cewa,

"Bayan aukuwar girgizar kasa, malamai sun tattara mu wajen kubutad da kanmu da kuma karatu. Ba kawai muna iya yin zama a cikin tantuna ba, har ma muna iya karatu a can. Mun gamsu da wannan."

Gao Siyuan, wata 'yar makaranta ta bayyana cewa, ko da yake muhallin karatu da zaman rayuwa ba su da kyau, amma za ta yi iyakacin kokarinta domin samun wani kyakkyawan maki a cikin jarrabawar da za a yi bayan wata guda. Kuma ta ce,

"Kowa zai samu matsin lamba daga jarrabawar neman shiga jami'a. Amma a wannan halin da ake ciki, za a kara samun karfi in yana da wani buri."

Ban da wannan kuma, a 'yan kwanakin nan da suka gabata, jami'o'i kusan 1400 na duk fadin kasar Sin da za su dauki dalibai a lardin Sichuan sun gabatar da shirye-shirye domin lura da dalibai masu neman shiga jami'a na yankunan da ke fama da bala'in. Wasu jami'o'i za su ci gaba da kara yawan daliban da za su dauka a yankunan da suka fi fama da bala'in bisa tushen kara yawan dalibai 'yan lardin Sichuan har kashi 2 cikin dari. Meng Qian, mai kula da ayyukan daukar dalibai na jami'ar Tsinghua ya bayyana cewa,

"Bisa tushen kara daukar dalibai na lardin Sichuan, jami'ar Tsinghua za ta gudanar da shirin musamman don daliban da za ta dauka daga yankuna masu fama da bala'in, wato za ta yi iyakacin kokari wajen daukar yawan daliban da suka dace."

Bugu da kari kuma, jami'o'i na biranen Beijing da Shanghai da kuma Guangdong sun tsai da kudurin samar da kudaden taimako ga dalibai masu fama da talauci na yankunan da ke fama da bala'in. Xu Jinwu, shugaban jami'ar kimiyya da fasaha ta Beijing ya bayyana cewa,

"Game da dalibai masu fama da talauci da suka zo daga yankunan masu fama da bala'in, jami'armu za ta biya dukkan kudadensu na karatu da zaman rayuwa da kuma zirga-zirga."(Kande Gao)