Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-25 15:32:59    
Waiwaye mafi kayatarwa a game da aikin ba da sharhi kan labarun wasannin motsa jiki

cri
Ray Hadley wani mai ba da sharhi kan labarun wasanni na musamman ne a kasar Australia. Shirin wasan kwallon zari-ruga na karshen mako da yake jan akalar filin ya fi jawo hakulan mutane a cikin shekaru 20 da suka gabata, akwai mutane kimani dubu 200 dake sauraron shirinsa a kowane kwata. Har sau 6 ne ya taba samu lambar yabo ta "mai ba da sharhi kan labarun wasanni mafi kyau a Australia". Mr. Ray ya taba yin aikin watsa labarun wasannin Olympic sau 4. To, yanzu, bari mu gabatar muku da wannan mai ba da sharhi labarun wasannin Olympic tare da wakilinmu dake Australia Chen Feng.

Jama'a masu sauraro, labarin da kuka saurara shi ne labarin da Ray Hadley ya yi a yayin da mai mika wutar wasannin Olympic ta Sydney kuma 'dan wasan Australia ta zama zakarar gasar gudun mita 400 ta mata a wasannin Olympic na Sydney. Duk domin Ray Hadley ya ba da sharhi ga wannan gasar, shi ya sa, gasar ta jawo hakulan mutane sosai. Mr. Ray mai shekaru fiye da 50 da haihuwa yana ganin cewa, ba zai manta da daren ran 25 ga watan Satumba na shekarar 2000 ba.

Tun daga shekarar 1992, Ray Hadley ya fara ba da sharhi labarun wasannin Olympic a matsayin mai ba da sharhi labarun wasannin Olympic, ya taba je biranen Barcelona da Atlanta da Athens, ba shakka, ya taba shiga cikin aikin ba da sharhi labarun wasannin Olympic na Sydney. Ya ce, ba da sharhi labarun wasannin Olympic na Sydney aikin musamman ne a gare shi. Yana mai cewa,

"Ko da yake, shekaru 8 sun wuce ke nan, amma a gare ni, ba da sharhi labaru a wasannin Olympic na Sydney ya zama aikin musamman sosai. Na tuna da cewa, a wancan lokaci, na fito daga gida da karfe 5 ko karfe 6 na safe a kowace rana, ina aiki har na tsawon awoyi 15 ko 16, tsawon lokacin da na ba da sharhi labaru a kowace rana ya kai awoyi a kalla 10."

A lokaacin da ake gudanar da gasar wasannin Olympic na Sydney, Mr. Ray ya dauki nauyin ba da sharhi labarun gasannin iyo da guje-guje da tsalle-tsalle. Ya siffanta aikinsa na kowace rana kamar haka: ya fara aiki da karfe 6 na safe, sa'an nan ya ba da sharhi labarun gasar iyo ta fid da gwani, sai kuma gasar guje-guje da tsalle-tsalle. Da dare, ya ba da sharhi gasannin karshe na iyo da guje-guje da tsalle-tsalle na karshe, ya kan kammala aikinsa da tsakar dare. Ko da yake ya gaji sosai, amma ya yi alfahari sosai. Mr. Ray ya ce, duk wanda ya iya yi iyakacin kokari a wancan lokaci zai iya nuna kwarewa.

Ray Hadley wanda ya gwanance sosai wajen ba da sharhi labarun wasanni zai zo birnin Beijing tare da abokan aikinsa a watan Agusta na shekarar bana, zai dauki nauyin ba da sharhi ga wasan iyo da guje-guje da tsalle-tsalle. Ya kiyasta cewa, kungiyar Australia za ta samu lambobin zinariya guda 5 zuwa 8. Duk da haka, Ray Hedley yana fatan 'yan wasan kasashe daban daban za su yi kyakkyawan aiki ba tare da samun mugun tasirin da sauran batutuwa ke kawo musu ba.

"Gasar wasannin Olympic muhimmiyar gasa ce, amma ba dandalin yin aikin siyasa ba. Mutane su taru a wuri guda ne duk domin wasanni, amma ba domin sauran abubuwa ba. A cikin makonni 2 da za a yi wasannin Olympic, ya kamata a kyale sauran batutuwan da ba su da nasaba da wasanni, hakan 'yan wasanni za su hada gwiwa don wasannin motsa jiki, kuma za su yi gasanni domin zaman lafiya da sada zumunta."