Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-25 15:19:16    
Ana cigiyar barawo ta yanar gizo ta internet a kasar Sin

cri
Mr Fan Hongwen,wani ma'aikaci ne na cin rani da ya ke aiki a birnin Kelamayi na jihar Xinjinag ta kabilar Uygur mai ikon tafiyar da harkokin kanta ya zo ne daga lardin Gansu,ya samar da wani hoton mai satar bankcard nasa a yanar gizo ta internet yana cigiyar mai sata.Mr.Fan y ace " na manta da daukar kati nawa bayan da na samu kudina daga injin ATM a ran 4 ga watan Yuni.Da na ba da rahoto kan bacewar katin ga ofishin 'yan sanda a ran 10 ga watan Yuni,na gano cewa an dauki kudina da ya kai kudin Sin Yuan dubu shida da dari daya.'yan sandan sun taimake ni da samun hoton mai satar katina ta film da aka dauka ta vidyo camera.ina fatan a sammance shi zan ba da kudin kyauta Yuan dubu daya ga duk wanda ya same shi.Fan bai samar da hoton mai sata a fili ba domin kare hakkinsa kan hoto,duk da haka masu amfani da yanar gizo ta internet suna so ya ba da ainihin hoton mai sata domin su ba da taimako.

Mutumin da ya samu jinya bai biya kudin asibiti ba. Kwanakin baya likitan fida a wani asibiti na jihar Xinjiang ta kabilar Uygur mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin ya kai karar wani mutumin day a samu jinya bai biya kudin asibiti ba. Likitan fida mai suna Li Gang ya yi wa wani mutum mai suna Yao Yunfeng fida yayin da ya ke samun rauni mai tsanani a kansa a ran 3 ga watan Maris da sassafe.Wani mutum daban da ya kai shi asibiti mai suna Xu a wannan lokaci ya ce shi da maras lafiya ba su da kudi,za su biya kudin asibiti bayan aka warkar da shi.Likitan fida Li Gang ya yi masa fida tare da nasara ya kubutar da shi daga hadari. Bayan kwanaki goma maras lafiya Yao Yunfeng ya bace ba tare da biyan kudin asibiti ba. Wani masani shari'a mai suna Kang Mingyuan ya bayyana cewa ya kamata a fakadar da jama'a kan zaman kamili mai fadi gaskiya da aikata gaskiya.haka kuma a inganta tsarin samar da magani ga jama'a.

Bakin gauraka masu dogon wuya sun yi sheka kusa da tafkin Qinghai na kasar Sin. Kwanan baya an gano gauraka masu dogon wuya kimani sama da sittin sun yi sheka dab da tafkin Qinghai na lardin Qinghai dake arewa maso yammacin kasar Sin. An ce wannan ne karo na farko da aka gano bakin gauraka masu dogon wuya da yawansu ba a taba gani ba sun yi sheka dab da tafkin Qinghai.wani jami'in hukumar kula da muhalli ta tafkin Qinghai ne ya fadi haka. Ya ce shekara bara wadansu gauraka ne kawai sun yi sheka dab da tafkin.

Wani manomi ya gina dakin tuanwa da mazajen jiya a kauyensa domin mutumta su. Kusan a kowace rana an sami maziyarta sama da dari da suka kai ziyara a dakin tunawa da mazajen jiya da wani manomi ya gina a kauyen Lianchi na gundumar Kaixian domin nuna girmamawarsu ga mazajen jiya da aka Haifa a kauyen nan wadanda suka bad a rayukansu ga sabuwar kasar Sin. Manomi Liu Yingde mai shekaru 68 da haihuwa ne ya yi amfani da daukacin kudin da ya ajiye a banki ya gina wannan dakin. Liu y ace yayin da yake yaro,ayyukan sadaukar da rain a mazajen jiya sun girgiza kaina,tun daga wannan lokaci in niyyata in gina wani dakin musamman dominsu.Ga shi a yau dakin tunawa da su ya shimfidu,ayyukansu na sadaukar da kai na ci gaba da yaduwa daga zuriya zuwa zuriya.