Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-23 15:14:27    
Na nuna sha'awa sosai ga birnin Beijing, a cewar likita na tawagar 'yan wasannin Olympics ta kasar Cape Verde

cri

An haifi Humberto Evora a kasar Cape Verde, kuma daya bayan daya ya taba koyon ilmin likitanci na motsa jiki a kasashen Portugal da Italiya. Daga baya kuma ya iso shiyyar Macao ta kasar Sin don gudanar da aikinsa. Sabo da nasarar da ya samu a fannin ilmin likitanci na motsa jiki, ya taba zama likita na tawagar 'yan wasa ta Macao da ta Cape Verde bi da bi bisa gayyatar da aka yi masa. A wannan karo, ya sake zuwa Beijing a matsayinsa na likita na tawagar 'yan wasa ta kasar Cape Verde. Kuma ya bayyana cewa, ya ji mamaki da sauyin Beijing in an kwatanta da yau da shekaru 18 da suka gabata. Kuma ya kara da cewa,

"Lokacin da na zo Beijing a wannan karo, na ji mamaki sosai da sauyin birnin. Na yi farin ciki kwarai da na iya ganin irin wannan sauyi. Yanzu ana iya samun hanyoyi da dama na jiragen kasa da ke tafiya a karkashin kasa a Beijing, wadanda za su ba da sauki ga tafiyar mazaunan wurin da masu yawon shakatawa."

Kuma Mr. Humberto ya bayyana cewa, a ko wane karo da ya zo Beijing, ya kan ga abubuwa daban daban. Kuma ya nuna sha'awa sosai ga al'adun Beijing musamman ma abincin Beijing. Ya kara da cewa,

"Dimbin 'yan kasashen waje da ba su taba zuwa Beijing ba suna ganin cewa, abincin Beijing ba shi da halin musamman ko kadan, amma a idona, abincin kasar Sin yana da iri daban daban, abincin Guangdong na kudancin kasar Sin da na Beijing sun sha bamban sosai. Abinci Beijing yana da dadin ci, kuma na taba dandana wasu daga cikinsu, kamar gasasshiyar agwagwa ta Peking, wadda ta kasance kamar wani irin abincin Beijing da ke da suna sosai. Amma ina ganin cewa, abincin Beijing ba gasasshiyar agwagwa ta Peking kawai ba, shi ya sa na ba da shawarar cewa, mutane masu yawon shakatawa suna iya zuwa dakunan cin abinci da ke kan tituna domin jin dadin abincin Beijing na gaskiya."

Ban da wannan kuma, Mr. Humberto ya gaya wa wakilinmu cewa, Beijing wani birnin ne da ke iya jawo hankulan mutane sosai. Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da ana kiyaye abubuwan gargajiya da yawa a cikin wannan babban birnin na zamani, kamar titin Hutong da tsarin gidajen kwana masu fasali 4 irin na da wato Siheyuan. Kuma ya kara da cewa, ya fi son Beijing da cike yake da sogogjin gargajiya idan an kwantata da abubuwan zamani na birnin, kuma ya ce,

"Na nuna sha'awa ga abubuwan gargajiya na Beijing, inda ake iya gano dogon tarihi da al'adu da kuma basirar Sinawa. Kana iya ganin wadancan abubuwan zamani a dimbin wurare, amma kana iya ganin wadannan abubuwan gargajiya a nan ne kawai, kuma wannan shi ne dalilin da ya sa dimbin mutanen kasashen waje suka zo Beijing don yin balaguro."

A Beijing, ko da rana ko da dare, har kullum Mr. Humberto yana iya samun abubuwa masu ban sha'awa. Kuma yana ganin cewa, Sinawa su kan nuna maraba da baki da hannu biyu biyu, yana iya samun dimbin abokai a Beijing. Ya ce,

"Da rana, na iya yin ziyara a gidajen ibada da dakunan nuna kayayyakin tarihi, kamar fadar sarakuna. Da dare kuma, na iya zuwa gidajen nishadi, inda halin annashuwa ya game ko ina, kuma mutane suke iya samun abokai. A ganina, 'yan birnin Beijing suna da budaddun zukata, ko da yake ana kasancewar matsalar harshe a tsakaninmu, amma muna iya yin zama kamar yadda ya kamata."(Kande Gao)