Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-17 19:08:21    
An rufe gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing, amma kauna da kulawa za su kasance har abada

cri

Yau, wato ran 17 ga wata da dare, za a rufe gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Bejing ta shekara ta 2008. Sabo da haka, yau da tsakiyar rana, a masaukin manyan baki na Diaoyutai, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya shirya wata liyafar cin abinci ta musamman domin maraba da manyan baki fiye da 30 wadanda suka zo daga kasashen duniya da kungiyoyin kasashen duniya a madadin gwamnati da jama'ar kasar Sin. A gun liyafar, Mr. Hu ya bayar da wani jawabi, inda ya bayyana cewa, tunanin "yin fice da haduwa da morewa" da aka bi a gun gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing ya zama wani kayan tarihi mai daraja ga wasannin motsa jiki na nakasassu. Gwamnatin kasar Sin da jama'arta za su ci gaba da yada tunanin mutumtaka kamar yadda ta saba yi wajen ciyar da wasannin motsa jiki na nakasassu da harkokin nakasassu na duk duniya gaba. Mr. Hu ya ce, "Yau da dare, za a rufe gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing. A madadin gwamnati da jama'ar kasar Sin, da hannu biyune, ina marhabin da dukkan manyan bakin da suka zo Beijing domin halartar bikin rufe gasar. Kuma cikin sahihanci ne mun nuna godiya ga dukkan abokan da suka bayar da gudummowarsu wajen shirya gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing cikin nasara. A waje daya, mun taya murna ga dukkan 'yan wasa na kasashe da yankuna daban daban da suka samu maki mai kyau a gun gasar."

A kan tarihin gasannin wasannin Olympic na nakasassu, wannan ne karo na farko ke nan da wani kwamitin shirya wasannin Olympic shi kadai ya shirya gasar wasannin Olympic da wata gasar wasannin Olympic ta nakasassu tare. A kwanan baya, an taba yin sharhin cewa, gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing ta kai al'ummar kasashen duniya wani sabo matsayi wajen kulawa da harkokin nakasassu. Manyan bakin da suka halarci liyafar da aka yi a yau da tsakiyar rana sun shaida hakan. Manyan baki fiye da 30 ciki har da Philip Craven, shugaban kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na kasa da kasa da matarsa da Jacques Rogge, shugaban kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa da matarsu da firayin minista Oumaru na kasar Nijer da shugabannin sauran kasashen duniya da na gwamnatocinsu sun halarci wannan liyafa, kuma za su halarci bikin rufe gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing. Lokacin da yake waiwayi wannan gasa, Mr. Hu ya ce, "A cikin kwanaki 12 da suka gabata, 'yan wasa nakasassun da suka zo daga kasashe da yankuna daban daban sun halarci ayyuka iri iri da aka shirya domin gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing. Sun kuma bayyana kwazonsu wajen kokarin neman cigaba kamar yadda suka rubuta wata wakar yaba wa rayuka mai kayatarwa. Jama'ar duk duniya, ciki har da na kasar Sin sun more nasara da farin cikin da aka samu a gun wannan gasar wasannin Olympic ta nakasassu."

Kafin wannan liyafa, Mr. Philip Craven, shugaban kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na kasa da kasa ya kira wani taron manema labaru, inda ya yaba wa gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing cewa, "gasa ce mai kayatarwa sosai da aka yi cikin nasara kwarai".

"Mai yiyuwa ne gasar wasannin Olympic ta nakasassu gasa ce mai kayatarwa da aka taba gani a karo na farko. Dukkan Sinawa sun shiga wannan gasa. Gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta karo na 13 wata gasar wasannin motsa jiki ce ta hakika."

A cikin zuciyar shugaban kasar Sin Hu Jintao, ba ma kawai gasar wasannin Olympic ta nakasassu gasar wasannin motsa jiki ce ta dukkan abokai nakasassu ba, har ma ita ce gagarumin bikin da ke bayyana yadda Bil Adam yake fice kansa, kuma ya more farin ciki. Mr. Hu ya ce, "Gwamnati da jama'ar kasar Sin za su yi amfani da wannan dama, kuma za su ci gaba da yada tunanin nuna mutumtaka kamar yadda suka saba yi domin ciyar da harkokin nakasassu na kasar Sin gaba. Kuma za su hada kan sauran gwamnatoci da jama'a na kasashen duniya wajen ciyar da harkokin nakasassu da wasannin motsa jiki na nakasassu na duniya gaba."   (Sanusi Chen)