Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-15 17:37:06    
Birnin Beijing ya yi kokarin daukar matakan samar wa nakasassu guraban aikin yi

cri

A cikin 'yan shekarun nan da suka gabata, cikin hali mai yakini ne birnin Beijing ya dauki matakai iri iri domin taimakawa nakasassu wajen samun aikin yi.

Ya kasance da nakasassu kusan miliyan 1 a birnin Beijing, wato ya kai kashi 6.5 cikin kashi dari bisa na jimlar yawan mutanen birnin. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, a cikin wadannan nakasassu, yawan mutanen da shekarunsu na haihuwa suke cikin lokacin yin aiki ya kai kimanin dubu dari 2, daga cikinsu yawan mutanen da suke son aiki ya kai kimanin dubu dari 1.

Mr. Li Shuhua, wanda ke jagorantar hadaddiyar kungiyar nakasassu ta birnin Beijing ya ce, gwamnatin birnin Beijing yana mai da hankali sosai kan yadda za a samar wa nakasassu guraban aikin yi. Mr. Li ya ce, "Bi da bi ne birnin Beijing ya bayar da manufofi masu gatanci fiye da 10 domin yin kokarin samar wa nakasassu guraban aikin yi. Bisa ka'idar samar wa nakasasshe dai dai gurabin aikin yi ko samar wa nakasassu masu dimbin yawa guraban aikin yi tare, ya bayar da manufofin sa kaimi ga kowane nakasasshe da ya samu aikin yi da kansa, ya yi kokarin samar da guraban aikin yi a cikin unguwoyin da nakasassu suke da zama. Sakamakon haka, nakasassu mai yawan gaske sun samu guraban aikin yi."

Mr. Ding Xiangyang, mataimakin magajin birnin Beijing ya amince da maganar da Mr. Li ya fadi. Mr. Ding ya gaya wa manema labaru cewa, yawan nakasassun da ya kai kashi 80 cikin kashi dari sun samu guraban aikin yi cikin nasara. Yawan kudin da birnin Beijing ya karba domin tabbatar da zaman rayuwar nakasassu ya kai kudin Renminbi yuan biliyan 1. Za a yi amfani da wadannan kudade wajen samar da guraban aikin yi ga nakasassu.

Madam Ping Yali, wadda ta samu lambar zinariya ta farko a gun gasar wasannin Olympic ta nakasassu, yanzu tana tafiyar da gidajen tausa na makafi 4. Ta gaya wa wakilinmu cewa, yanzu akwai gidajen tausa na makafi kusan dari 3 a Beijing. Gwamnatin birnin Beijing ta tallafa wa nakasassu wajen kafa wadannan gidajen tausa domin kiyaye su da samar da guraban aikin yi ga makafi. Madam Ping ta ce, "Idan mun bi dokoki da manufofi, kuma muka mai da hankali kan nakasassu da kyau, za mu iya samun tallafin kudi daga asusun tallafawa nakasassu. An karbi irin wadannan kudade ne daga hukumomi da bangarori daban daban domin tabbatar da zaman rayuwar nakasassu. Ana kuma ba mu wasu injuna da na'urorin da muke bukata."

1 2