Bayan da aka soma gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing a ran 7 ga wata, wasu 'yan wasa nakasassu sun samu maki mai kyau. Alal misali, Natalie Du Toit, 'yar wasa nakasashiyya ta kasar Afirka ta kudu wadda ta taba shiga gasar wasannin Olympic ta Beijing ta samu wata lambar zinariya a gun gasar wasan ninkayya ta salon malam-bude-littafi ta mita 100 da aka yi a ran 7 ga watan Satumba, ta kuma kafa wani sabon matsayin bajinta na duniya a gun wannan gasa.
A ganin Natalie Du Toit, wannan lambar zinariya tana kasancewa a cikin zuciyarta tamkar matsayi na 16 da ta samu a gun gasar wasan ninkayya ta kilomita 10 ta wasannin Olympic na Beijing.
1 2 3 4
|