Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-09 15:22:34    
Filayen wasa na wasan Olympic a jami'o'in da ke nan Beijing(3)

cri

In wani yana tukin mota a kan hanya ta 4 a gabas da ta zagaya birnin Beijing, tabbas ne zai lura da wani ginin da ya yi kama da wani kwallon badminton, shi ne babban dakin wasa kacal da aka gina a kudu maso gabashin Beijing, wato dakin wasa na jami'ar koyon ilmin masana'antu ta Beijing. Wannan dakin wasa zai dauki bakuncin gasannin wasan kwallon badminton da wasan salon lankwashe jiki wato wasan eurythmics a Turance. An soma gina wannan dakin wasa a ran 30 ga watan Yuni na shekarar 2005, inda akwai kujeru dubu 7 da dari 5 a ciki. Siffar dakin wasan ta yi kama da wani kwallon badminton. Manyan igiyoyin bakin karfe guda 5 da suka alamta zobba 5 na wasan Olympic suna kewayen rufin gilas na wannan dakin wasa, sa'an nan kuma, an hada su da wasu igiyoyin bakin karfe guda 56 da suka alamta kabilu 56 na kasar Sin.

Gina dakin wasa na gasar wasannin Olympic a jami'ar koyon ilmin masana'antu ta Beijing ya bai wa wannan jami'a mai dogon tarihi, wadda kuma ta shahara saboda nazari da kuma koyar da ilmin injiniya wata dama mai daraja. Da farko dai, ba a bukatar gayyatar sauran masu zayyana, saboda jagororin nazarin tsarin bakin karfe na jami'ar su ne suka zayyana dakin wasa kai tsaye. Dalibai masu neman samun digiri na 2 kuwa sun dukufa kan yadda za a kyautata tsarin bakin karfe. Wadannan dalibai da ke karatu a jami'a ba kawai sun kammala gwajin da abin ya shafa tare da malamansu kafin a fara gina wannan dakin wasa ba, har ma sun shiga ayyukan tsara shirin kyautata tsarin bakin karfe. Ko da yake suna karatu a jami'a, amma sun shiga ayyukan zayyana gine-gine na zamani a duniya, tabbas ne wadanda shekarunsu ya yi daidai da wadannan dalibai za su yi hassada da su sosai.

Bayan gasar wasannin Olympic ta Beijing, wannan dakin wasa zai kasance a matsayin cibiyar motsa jiki ga dukkan dalibai da malaman koyarwa na jami'ar ilmin masana'antu ta Beijing, haka kuma za a bude shi ga mazaunan wurin. Bugu da kari kuma, wannan dakin wasa zai ci gaba da kasancewa a wannan kyakkyawar jami'a, a wannan birni a matsayin kayan tarihi na al'adu mai daraja.

Yanzu bari in yi muku bayani kan dakin wasa na karshe na gasar wasannin Olympic da aka gina a cikin jami'o'in Beijing, wato dakin wasa da ke cikin jami'ar ilmin kimiyya da fasaha ta Beijing, inda za a yi gasanin Judo da Taekwondo a shekara mai zuwa. Akwai kujeru dubu 8 a cikin dakin wasan. Jami'ar ilmin kimiyya da fasaha ta Beijing wata jami'a ce daban da ta gwanance a fannin ilmin injiniya, shi ya sa masu zayyana suka mai da hankulansu kan tabbatar da amfanin wannan dakin wasa, a maimakon siffarsa ta zamani. An samar da tsarin ba da haske a cikin dakin wasan bisa sabuwar fasaha. Bayan da aka yi amfani da wannan sabuwar fasaha, an shigo da hasken rana domin tabbatar da ba da haske na tsawon awoyi 10 a cikin wannan dakin wasa da rana, sa'an nan kuma, ba a bata albarkatu ko kadan ba. Bugu da kari kuma, hasken rana da ake shigowa ya iya kawar da warin da ke cikin dakin, ta haka za a kiyaye lafiyar mutanen da ke cikin wannan dakin wasa.