Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-08 21:29:34    
Sin na dinga daukaka cigaban sha'anin nakasassu

cri

Jama'a masu saurare, yau dai an gudanar da wani taron yada labarai a babbar cibiyar watsa labarai ta gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing, inda mataimakin babban shugaban hadaddiyar kungiyar nakasassu ta kasar Sin Mista Sun Xiande ya furta cewa, sha'anin nakasassu na kasar Sin ya rigaya ya yalwata har ya zama wani sha'anin zamantakewar al'umma dake shafar fannoni daban-daban maimakon sha'anin shimfida zaman jin dadi kawai. Gwamnatin kasar Sin ta dauki jerin kwararan matakai don ingiza yunkurin bunkasa sha'anin nakasassu na kasar. Hakan ya kyautata yanayin rayuwar nakasassu a bayyane.

Wani sakamakon binciken da aka yi a karo na biyu ga nakasassun duk kasar, an ce, a yanzu haka dai, kasar Sin na da nakasassu sama da miliyan 80, wadanda suka dauki sama da kashi 6 cikin kashi 100 na mutanen duk kasar. A matsayin wani gungun musamman, lallai ayyukan bada tabbaci ga hujjoji da fa'ida na nakasassun kasar Sin sun fi daukar hankulan bangarori daban-daban na al'ummomin kasar. Mista Sun Xiande ya fada wa wakilinmu cewa : ' A cikin shekaru fiye da goma da suka gabata, gwamnatin kasar Sin ta dauki jerin tsauraran matakai. Hakan ya kyautata yanayin rayuwar nakasassu a bayyane. Har sau biyu ne aka gudanar da bincike ga nakasassu a fadin duk kasar, da kaddamar da ' Doka kan bada tabbaci ga nakasassu', da ' Ka'idoji kan bada ilmi ga nakasassu' da kuma ' Ka'idoji kan samun aikin yi na nakasassu' da dai sauran dokokin shari'a ; Ban da wannan kuma, an aiwatar da shirye-shirye guda biyar na gwamnatin kasar kan ayyukan bunkasa sha'anin nakasassu, da kafa hukumomin aiki na gwamnati mai kula da harkokin nakasassu, da tsara manufofin dake shafar fannin shawo kan ciwace-ciwace, da bada ilmi, da samar da aikin yi da kuma na bada tabbaci ga zamantakewar al'umma da dai sauran fannoni, da kafa dinkakkun kungiyoyin nakasassu irin na sabon salo, har da gudanar da harkokin tallafa wa nakasassu daga dukkan fannoni.

A gun taron watsa labarai, Mista Yu Faming, shugaban sashen kula da harkokin albarkatun kwadago da na bada tabbaci ga zamantakewar al'umma na kasar Sin ya bayyana cewa :' Ya zuwa karshen shekarar da ta gabata, yawan nakasassun da suka samu aikin yi a birane da garuruwa na fadin duk kasar ya rigaya ya kai 433,700 ; kuma manoma nakasassun da suka samu aikin yi sun kai miliyan 16 da 966,000 ; Kazalika, yawan karin naskasassu da akan samu a birane da garuruwa na kasarmu ya kai kimanin 300,000, wadanda akasarinsu suka samu aikin yi '.

Jama'a masu saurare, domin kara inganta sha'anin nakasassu, bangarorin kula da harkokin jama'a na kasar Sin sun gudanar da dimbin harkokin tallafa wa nakasassu. Wani babban jami'in kula da ayyukan jin kai na kasar Sin, Mista Zhang Shifeng ya furta cewa : ' A 'yan shekarun baya, ma'aikatar kula da harkoin fararen hula ta kasar Sin na mai da hankali sosai kan ayyukan raya hukumomin zaman jin dadi na birane da garuruwa. Kuma nan da 'yan shekaru masu zuwa, za a kafa wata cibiyar jin dadin jama'a ciki har da nakasassu a kowace gunduma, da kowace jiha da kuma kowane birnin kasar'.

A karshe dai, Mista Xun Xian de ya furta cewa, an rigaya an samu cigaban a-zo-a-gani wajen fadakar da jama'a a game da ayyukan tallafin nakasassu. ( Sani Wang )