Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-08 15:27:56    
Labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri

---- Kwanan baya, an bude wurin yawon shakatawa na kwarin dutse mafi girma na duniya wato babban kwarin Yarlung Zangbo a hukunce. Kamfanin yawon shakatawa na jihar Tibet shi ne ya ware kudin sin wato Yuang miliyan 350 domin gina wannan wurin yawon shakatawa mai muhillin halittu mafi girma na kasar Sin wanda kuma ke hade da dakunan cin abinci da wurin kwana da na yawon shakatawa.

Babban kwarin dutse na Yarlung Zangbo da aka bude a wannan gami yana yankin Linzhi na jihar Tibet, duk tsawonsa ya kai kilomita 130. A wannan wurin yawon shakatawa, da akwai cikakken tsarin halittu masu rai na tuddai, da wurare masu ni'ima na halittu da na al'adun gargajiya ciki har da tsaunukan da ke rufe da dusar kankara da tatsuniyoyi addinai daban-daban.

A halin yanzu, an riga an gama dukkan ayyukan gine-gine da ke wurin yawon shakatawa na babban kwarin Yarlung Zangbo, kuma ana an fara aiki da su.