Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-08 15:26:30    
'Yan makarantar midil na kabilar Tibet da ke karatu cikin makarantar midil da ke karkashin jimi'ar Shanxi

cri

Domin kara tallafin kwararrun mutanen jihar Tibet da kyau, daga shekarar 1985, gwamnatin kasar Sin ta fara zabar wasu makarantun midil masu kyau wajen halayyar malaman koyarwa da sharudan ba da ilmi daga larduna da birane 19 na cikin kasar, wadamda suka bude azuzuwa musamman domin 'yan makarantun midil da suka zo da jihar Tibet. Makarantar midil dake karkashin jami'ar Shanxi da ke birnin Taiyuan, hedkwatar lardin Shanxi ta bude azuzuwa 6 wadanda suke daukar 'yan makarantar midil 400, wadanda kuma dukkansu suka zo ne daga jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta. To, jama'a masu sauraro, cikin shirinmu na yau za mu ba ku labari dangane da wadannan 'yan makarantar midil na jihar Tibet wadanda suke karatu cikin makarantar midil dake karkashin jami'ar Shanxi.

"Ga inuwarki mai tsit cikin hasken wutar lantarki, babu isassun maganganun da zan iya fada don bayyana irin kaunar da kike nuna mini, ki taimake ni bisa hanyar da nake bi domin zama kwararre. Ya malama, ke ce dangina mafi kusanci tun bayan da na bar garina, kuma ke ce uwarmu ta tarayya."

Wannan uwar tarayya da ke cikin zukatan yara ita ce madam Bai Donghong, malamar da ke kula da ajin 'yan makaranta na Tibet gaba daya. Malama Bai wata tsohuwar malama ce wadda ta shafe fiye da shekaru 30 tana aikin koyarwa, tun daga shekarar 1985 wato lokacin da majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta danka wa makarantar midil da ke karkashin jimi'ar Shanxi nauyin bude ajin 'yan makaranta na jihar Tibet zuwa yanzu, malama Bai ta zama malama ta farko wadda ta ke kula da ajin gaba daya.

Yanzu da akwai 'yan makaranta 41 cikin ajin da malama Bai take koyarwa, malama Bai kuma ta ba da babban taimako ga kowanensu, ta ce,

"Ina jin cewa, wadannan 'yan makaranta sun yi tamkar 'ya'yana, kowanensu ina son sa. Dukkansu suna kaunar kungiyar tarayya, da neman daukaka kwarjinin ajinsu, alal misali, sun taba shiga gasar rera wakoki da yin raye-raye, duk irin gasannin da suka halarta, sukan samu lambobin yabo na mataki na farko na makarantar."

Domin taimaka wa wadannan yara 'yan makarantar midil na kabilar Tibet da su kamalla aikin karatunsu lami lafiya, da rage nauyin matsin lambar da ake yi wa iyayensu wajen tattalin arziki, gwamnatin lardin Shanxi takan shigar da kudin Sin wato Yuan 300 cikin katunan cin abinci na kowane 'yan makarantar kabilar Tibet a kowane wata, kuma tun tuni an daidaita matsalar duba likita ga wadannan 'yan makaranta ta hanyar kafa tsarin inshorar lafiya a jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta.

Yarinya Dawa Drolma tana daya daga cikin 'yan makaranta na ajin kabilar Tibet, ba ma kawai ta iya rera waka sosai ba, kuma tana da kyau kwarai. Da farko ba ta son yin magana da abokan karatunta, daga baya bisa kwarin gwiwar da malaman koyarwa da abokan karatu suka yi mata, yarinya Drolma ta fara cika imani ga kanta, kuma takan nuna farin ciki. Ta yi rajistar shiga gasanni daban-daban a gun bukukuwan fasasa da kimiyya da Sinanci da Turanci da makarantar ta shirya, sabo da haka ba ma kawai ta samu ci gaba wajen nuna jan hali cikin zaman yau da kullum ba, kuma ta samu karuwa da yawa. Abin da ya fi shiga mata zuci shi ne gasar da aka yi a farkon lokacin shigowarta cikin makarantar domin zaben mawaka mafi kyau guda 10, ta tuna da cwa,

"Lokacin da na hau kan dandalin wasa a karo na farko, ina jin tsoro kwarai, hannuna yana dauke da makarufo kuma yana rawa. Na ga 'yan makaranta na ajin kabilar Tibet dukkansu sun zo wurin gasar, kuma sun yi mini tafin hannu bayan da na rera jumla daya ko 2 na wakar, wannan lalle ya burge ni kwarai, ba zan manta da shi ba cikin zaman rayuwata."

Cikin shekaru 23 da suka wuce, makarantar midil dake karkashin jami'ar Shanxi ta riga ta tallafa 'yan makarantun sakandare da na midil wadanda yawansu ya kai 1,600 domin jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta, daga cikin su kuwa da akwai mutane kusan 1,000 wadanda suka koma jihar Tibet kuma suka samu aiki a can.