Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-05 22:07:02    
Beijing a shirye yake wajen gudanar da gasar wasannin Olympic ta nakasassu

cri

Beijing ta sami nasarar gudanar da gasar wasannin Olympic cikin adalci ba tare da yin amfani da magani mai sa kuzari ba. Wang Wei ya nuna cewa, za a ci gaba da bincike magani mai sa kuzari a cikin gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing a tsanake kuma yadda ya kamata, za a yi namijin kokari wajen samar wa 'yan wasa dandamalin yin takara cikin adalci. Ya ce,'Za mu yi bincike kan samfurin fitsari ko na jini 1100 a cikin wannan gasar wasannin Olympic ta nakasassu, yawan samfurin zai fi na Athens da kashi 70 cikin dari. Ya kai matsayin koli a tarihin gasar wasannin Olympic ta nakasassu. Za a kuma bi matakan bincike mafiya tsattsaura. A lokacin gasar wasannin Olympic ta nakasassu, masu bincike 480 za su yi aiki a dukkan tasoshin bincike a karkashin sa ido da kwamitin yaki da magani mai sa kuzari na kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na duniya da kuma 'yan kallo masu zaman kansu na hukumar yaki da magani mai sa kuzari ta duniya za su yi.'

Mr. Wang yana fatan dukkan kokarin da Beijing ke yi zai bai wa nakasassun da za su zo Beijing farin ciki. Beijing a shirye yake. Ya ce,'Tun daga filin jirgin sama da baki za su sauka, da motocin da za su shiga da kuma otel-otel da wuraren nishadi da wuraren yawon shakatawa da sauran abubuwa a shirye suke baki daya. Babu tantama za mu ci gaba da wasu ayyuka, amma a galibi dai, Beijing a shirye yake wajen karbar 'yan wasa da 'yan kallo nakasassu.'(Tasallah)


1 2