Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-04 22:16:53    
Wasannin Olympic na nakasassu kasaitaccen biki ne da ke kawo wa 'yan Adam zaman lafiya da zumunci

cri

Saurari

Douglas Sidialo shugaba ne na kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na kasar Kenya. Kwanan baya, yayin da Mr.Sidialo ke ziyara a kauyen wasannin Olympic na nakasassu na Beijing, ya nuna babban yabo ga yadda ake share fagen wasannin Olympic na nakasassu. kyakkyawan yanayin zama da ke kauyen wasannin Olympic na nakasassu da rashin abubuwan cikas ga nakasassu da kuma ayyukan masu aikin sa kai sun burge Mr.Sidialo sosai, ya ce, "Kauyen wasannin Olympic na nakasassu yana da kyaun gani sosai. Mutanen wurin na karbar baki da hannu biyu biyu, kuma an shirya kome da kome yadda ya kamata. Na kai ziyara ga dakin cin abinci da dakunan kwana na 'yan wasa, ma iya cewa, ba su da aibi."

Kenya ta tura wata tawagar da ke kunshe da mutane 27 zuwa wasannin Olympic na nakasassu da za fara a birnin Beijing, ciki har da 'yan wasa 13, wadanda za su shiga gasannin guje-guje da tsalle-tsalle da daga nauyi da dai sauransu. A lokacin da yake magana a kan burin da 'yan wasan Kenya ke neman cimmawa a gun wasannin Olympic na nakasassu na Beijing, Mr.Sidialo cike yake da imani, ya ce, " 'yan wasa nakasassu na Kenya suna da karfi a wasan guje-guje da tsalle-tsalle, kuma muna sa ran samun nasara a gasar gudun dogon zango na maza. Ko da yake 'yan wasa nakasassu da za su shiga wasannin guje-guje da tsalle-tsalle a wannan karo ba su da yawa, amma za su yi kokari a gun gasanni. Ina imani da cewa, za su jawo wa Kenya alfarma."

1 2