Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-02 20:26:15    
Filayen wasa na wasan Olympic a jami'o'in da ke nan Beijing (babi na daya)

cri

'Bayan da aka kammala kafa dakin wasa na jami'armu, to, za mu mallaki dakin wasan kwallon tebur mafi kyau a duniya.' daliban jami'ar Beijing su kan fadi hakan cikin alfahari. A shekarar 2008, a jami'ar Beijing ne za a yi gasar wasan kwallon tebur, wadda irin wasa ne da Sinawa suka fi jin alhafari kansa. An fara gina dakin wasan kwallon tebur na wasan Olympic a jami'ar Beijing tun daga ran 19 ga watan Yuli na shekarar 2005, inda akwai kujeru din din din dubu 6 da kuma na wucin gadi guda 2000 a ciki.(music)

In kun zagaya dakin wasan, to, mai yiwuwa ne za ku ji mamaki sosai, saboda wannan dakin wasa mai kusurwoyi 4 an yi masa kusurwa kadan domin kada a tura tsofaffin bishiyoyi 7 da kuma wani karamin lambu irin na daular Qing ta kasar Sin. Mene ne dalilin da ya sa hakan?

A zahiri kuma, bisa shirin da aka tsara a da, masu zayyana sun yi shirin sake gina wannan karamin lambu a wani wuri daban mai fadi bisa yadda yake a da. Amma duk da haka, a lokacin da wani dalibin jami'ar yake waiwaya bayanan tarihi, ya ji mamaki saboda gano cewa, a gaskiya kuma, wannan karamin lambu wani bangare ne kacal na wani babban lambun daular Qing, kuma har zuwa yanzu yana kasancewa. Tsoffin bishiyoyi 7 da ke waje da shi kuwa an dasa su a lokacin, wato yau shekaru fiye da 200, a cikinsu kuma, mafi tsoho shekarunsa ta wuce 200 da haihuwa. Malamai da dalibai sun mika rahoto kan wannan lamari ga hukumar kula da kayayyakin gargajiya ta Beijing, ta haka, hukumomin da abin ya shafa sun tsai da kudurin kiyaye kayayyakin gargajiya da aka samu a wanann wuri.

Amma saboda haka ne, ba yadda za su yi, sai wadannan masu zayyana sun sake zayyana wannan dakin wasa. Domin kiyaye saiwoyin wadannan tsoffin bishiyoyi 7, an sake gina rassan dakin wasan da ke karkashin kasa a wurin da ke da nisan mita 3 a kudu daga asalin wurin da aka gina shi. Sa'an nan kuma, an sake hada dimbin bututun da ke karkashin kasa. Ban da wannan kuma, don magance saiwoyin wadannan tsoffin bishiyoyi su rasa isasshen ruwa, shi ya sa masu zayyana gine-gine suka kebe wurin ajiyr ruwa a karkashin kasa a tsakanin tsoffin bishiyoyin da kuma dakin wasa.

A sakamakon ci gaban ayyukan gina dakin wasan, an kafa kwaurin rufi a kan tsoffin bishiyoyin da ke kusa da dakin wasan, ta haka, za a hana kayayyakin gine-ginen da suka fada daga sama su yi wa tsoffin bishiyoyin barna.

Ko da yake irin wadannan matakai sun kashe kudade da yawa, amma bayan shekarar 2008, dukkan mutane za su iya gani a cikin jami'a mafi tsufa a kasar Sin, wannan sabon dakin wasa zai yi zaman tare da wuraren gargajiya na al'adu na tsawon shekaru misalin 200 cikin jituwa.