Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-02 20:20:10    
Dalilin da ya sa aka gyara yawan karfin digiri na girgizar kasa

cri

A 'yan kwanakin nan da suka gabata, bayan da aka yi bincike kan bayanan da abin ya shafa, hukumar girgizar kasa ta kasar Sin ta gyara yawan karfin digiri na mummunar girgizar kasa da ta auku a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin daga 7.8 zuwa 8 bisa ma'aunin Richter. To wane abu ne da aka dogara wajen yin haka? Kuma mene ne ma'anarsa? Masu sauraro, a cikin shirinmu na yau, za mu yi muku wani bayani kan batun.

Hanya ce da a kan bi kullum wajen bincike da kuma tabbatar da yawan karfin digiri na girgizar kasa a duk duniya ita ce bayan aukuwar girgizar kasa, da farko manazarta su ba da rahoto kan girgizar kasa cikin sauri bisa bayanan sanya ido da suka samu daga tashar kula da girgizar kasa da ke kusa da cibiyar girgizar kasa, daga baya kuma sun tattara labarai daga dukkan fannoni domin kara yin bincike.

Sun Shihong, wani manazarci na cibiyar girgizar kasa ta kasar Sin ya bayyana cewa, ta wannan hanya, ana iya sanar da lokaci da kuma wuraren aukuwar girgizar kasa ga gwamnati da fararen hula a cikin lokaci mafi gajere domin gudanar da ayyukan ceto cikin lokaci. Amma za a gamu da matsala wajen yin haka, wato bayanan sanya ido na farko kan karfin digiri na girgizar kasa ya sha bamban da wanda aka samu bayan da aka yi bincike sosai. Kuma ya kara da cewa, "Yanzu ma'aunin tabbatar da yawan karfin digiri na girgizar kasa da muke yin amfani da shi wani matsakaicin yawan karfin digiri ne, wato wata matsakaciyar jimla ce da muka samu daga tashoshin kula da girgizar kasa daban daban. Idan mun samu tashoshin da yawa, to matsakaiciyar jimlar karfin digiri da muka samu a karshe za ta sha bamban."

Haka kuma an yi aikin tabbatar da yawan karfin digiri na girgizar kasa da ta auku a gundumar Wenchuan ta kasar Sin kamar haka. A ran 12 ga wata, bayan aukuwar girgizar kasa, tashar kula da girgizar kasa ta birnin Chengdu da ya fi kusa da cibiyar girgizar kasa ta samu alamar girgizar kasa a cikin dakika shida. Kuma bayan minti guda, tsarin daidaita girgizar kasa na cibiyar girgizar kasa ta kasar Sin ta yi gangami, kuma an tabbatar da yawan karfin digiri na wannan girgizar kasa bayan mintoci da dama. A ran 18 ga wata, bisa ka'idojin kasashen duniya, hukumar kula da girgizar ta kasar Sin ta yi amfani da labarun da ta samu daga tashoshin kula da girgizar kasa wajen yin bincike sosai kan wannan girgizar kasa, kuma a karshe dai ta gyara yawan karfin digiri na girgizar kasa zuwa 8 bisa ma'aunin Richter. Sun Shihong ya gaya mana cewa, "Mu kan yi musanyar labarun girgizar kasa tare da wasu tashoshin kula da girgizar kasa na kasashen duniya, kamar kasashen Australia da New Zealand da kuma Amurka da dai sauransu. Kuma mun gyara yawan karfin digiri na girgizar kasa ta wannan karo ne bisa labarun wasu tashoshi na kasa da kasa."

Ban da wannan kuma Mr. Sun ya kara da cewa. Karfin digiri na girgizar kasa wani ma'auni ne wajen tabbatar da karfin girgizar kasa. Ko da yake jimloli 7.8 da 8 ba su sha bamban sosai bisa ma'ana ta fuska, amma sun sha bamban kwarai da gaske wajen bayyana karfin girgizar kasa. Kuma ya ce, "Yin girgizar kasa mai karfin digiri 8 sau daya ya yi daidai da yin girgizar kasa mai karfin digiri 7.8 har sau da dama."

Wannan girgizar kasa da ta auku a lardin Sichuan ta samar ta shafi birane da larduna fiye da 10 na kasar Sin da kuma kasashen Vietnam da Thailand bisa matsayi daban daban. Kuma bisa kwarya-kwaryar kididdigar da aka bayar, an ce, wannan girgizar kasa ta lallata yankunan kasar Sin da fadinsu ya zarce murabba'in kilomita dubu 100 sosai.