Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-01 21:42:05    
Gasar Olympic za ta zama wata gasar Olympic mafi nasara a tarihi

cri

A kwanan baya, bisa gayyatar da shugaban gidan rediyon kasar Sin, wato CRI ya yi masa ne, Mr. Mark Thompson, shugaban kamfanin BBC ya zo Beijing don kallon bikin kaddamar da gasar Olympic ta karo na 29 a nan birnin Beijing. A kwanan baya, lokacin da yake ganawa da wakilinmu, Mr. Thompson ya bayyana cewa, tabbas ne gasar Olympic ta Beijing za ta zama wata gasar Olympic mafi kyau a tarihi.

Lokacin da Mr. Mark Thompson yake ziyara a gidan rediyon kasar Sin a kwanan baya, ya ce, yana jin alfahari sosai sabo da ya samu damar kallon bikin kaddamar da gasar Olympic ta Beijing bisa gayyatar da CRI ya yi masa. Ya kara da cewa, ko da yake kowane bikin kaddamar da gasar Olympic da aka taba yi a da yana da halinsa na musamman, amma bikin kaddamar da gasar Olympic ta Beijing ya jawo hankulan 'yan kallo na kasar Britaniya da na sauran kasashen duniya sosai.

"Ina cike da imani cewa, wannan biki zai ba mu alama sosai. Ana mamaki sosai ga albarkatun kwadago da shirye-shiryen da ke kunshe da al'adu da fasahohin zane-zane da aka nuna a gun bikin. Na iya tabbatar da cewa, jama'ar sauran kasashen duniya za su kara samun sha'awa kan kasar Sin."

A waje daya kuma, Mr. Mark Thompson ya ce, bayan da BBC ya samu izinin wasta labarun gasar Olympic ta Beijing, yau da shekaru 6 ko 7 da suka gataba, kamfanin BBC ya soma aikin share fagen watsa labarun gasar Olympic ta Beijing. Kamfanin BBC ya aika da ma'aikata fiye da dari 4 zuwa kasar Sin domin watsa labarun gasar Olympic ta Beijing, kuma yawan shirye-shiryen da kamfanin BBC zai watsa zai kai kusan sa'o'i dubu 3. Bugu da kari kuma, a birnin London da sauran wuraren duniya, darurukan ma'aikatan BBC suna watsa labarun da suke da nasaba da gasar Olympic ta Beijing.

Mr. Thompson ya kara da cewa, kafofin watsa labaru na kasashen duniya dukkansu suna mai da hankali sosai kan aikin watsa labarun gasar Olympic. Ya ce, ya kamata kafofin watsa labaru su yi kokari wajen sa kaimi kan jama'ar kasashe daban daban da su yi mu'ammala da juna da fahimtar juna. Idan kafofin watsa labaru sun watsa labaru da shirye-shiryen da suke bayyana hakikanin zaman rayuwar jama'a na kasashe daban daban bisa halin da ake ciki, jama'ar kasashe daban daban za su iya kara fahimtar juna da jure wa juna. Daga karshe dai, za a iya kawo wa duniyarmu zaman lafiya da zama mai jituwa.

"A ganina, wani muhimmin nauyin da ke bisa wuyan kafofin watsa labaru shi ne kara yin mu'ammala da fahimtar juna a tsakanin jama'ar kasashe da yankuna daban daban. Wannan ra'ayi yana dacewa da tunanin da aka bayar a gun gasar Olympic ta Beijing."

Bugu da kari kuma, Mr. Thompson yana ganin cewa, ya kamata kafofin watsa labaru su yi kokarin watsa labarun da suke shafar batutuwan da bil Adam suke fuskanta tare, kamar batun sauyin yanayin duniya da batun muhalli.

"A ganina, ya kamata kafofin watsa labaru da ke watsa shirye-shirye a duk fadin duniya su taka muhimmiyar rawa wajen sanarwa yankunan duniyarmu cewa, muna da moriya daya. Mai yiyuwa ne ya kasance da wasau sabane-sabane a tsakaninmu, amam muna da dimbin kwatankwacin moriya."

Mr. Thompson ya kuma gaya wa wakilinmu cewa, lokacin da kasar Sin take samun cigaban tattalin arziki, kuma tana ta yin tasiri a duniya, yanzu yawan matasan kasar Britaniya da suke koyon harshen Sinanci yana karuwa, dansa ma yana daya daga cikinsu. Lokacin da ya kawo wa kasar Sin ziyara a kowane lokaci, ya kan yi mamaki sabo da sauye-sauyen da kasar Sin ke samu cikin sauri kwarai.

"Za ka iya ganin sauye-sauyen da suke faruwa a gaban idonka. Idan ka zo kasar Sin bayan shekaru 2 masu zuwa, za ka ga an riga an samu sauye-sauye kwarai. Ina jin alfahari sosai domin kawo wa kasar Sin ziyara a wannan lokacin da ake soma gasar Olympic ta Beijing wadda take burge mu kwarai."

Mr. Thompson ya kara da cewa, gasar Olympic wani kasaitaccen biki ne da ke yin mu'ammala da koyi da juna a tsakanin al'adun yamma da gabashin duniya. Za ta iya taka rawa wajen sa kaimi kan mutane da su samu ilmi da yin musanye-musanye a tsakaninsu. Daga karshe dai Mr. Thompson yana fatan gasar Olympic ta Beijing za ta ci nasara. (Sanusi Chen)