Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-01 20:22:25    
Sabon zaman rayuwar da ake yi a kauyen Sangmo da ke kewayen birnin Lhasa

cri

Kauyen Sangmo wani kauyen yawon shakatawa ne na fannin al'adu da ke kewayen birnin Lhasa na jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin, kauyen yana yammacin birnin Lhasa, nisan dake tsakaninsa da birnin kuma ya kai kilomita 40. To jama'a masu sauraro, cikin shirinmu na yau za mu raka ku kai ziyara a wannan kauye don ganin yadda mutane suke zaman jin dadi a can.

A ran 21 ga watan Yuni da ya wuce da safe, an mika wutar wasannin Olimpic a birnin Lhasa na jihar Tibet, 'yan kabilar Tibet na kauyen Sangmo sun ci ado kuma suna wake-wake da raye-raye domin maraba da zuwan wutar, wata tsohuwa mai sunan Yangzom wadda ta ba shekaru 87 baya ta gaya wa wakilinmu cewa, "Na tsabtace gidana sosai, ga furannin da ke farfajiya sun tohu, kuma suna da kyaun gani. Ni ma na shirya farin kyallen da ake kira Hada, da giyar da aka yi da sha'ir don yin maraba da zuwan mutane masu mika wutar wasannin Olimpic."

Kauyen Sangmo inda tsohuwa Yangzom take zama wani wuri ne da ya shahara wajen wake-wake da raye-raye. A shekarar 2002, birnin Lhasa ya tsai da cewa, kauyen Sangmo ya zama kauyen yawon shakatawa wajen al'adu na jihar Tibet. Bisa matsayinta na mawakiya, kuma mai yin jagorancin masu yawon shakatawa wadda ta fi yawan shekaru da haihuwa a kauyenta, tsohuwa Yangzom ta yi suna a wurin, mutanen da suka zo kauyen domin yawon shakatawa dukkansu suna son jin wakokin gargajiya da kwaikwayon Tibet da ta rera.

Jama'a masu sauraro, wakar da kuka saurara dazu wata wakar gargajiya ce mai sunan "Drolmalakang" da tsohuwa Yangzom ta rera ta samu karbuwa ko'ina daga jama'ar jihar Tibet. A cikin wakar da ta rera tana cewa, "Tuddan da ke garinmu sun fi kayatarwa, ruwan da ke garinmu ya fi tsabta, mutanen garinmu kuma suna da kirki da sahihanci."

Tsohuwa Yangzom tana zama a kauyen Sangmo, a cikin harshen kabilar Tibet, kalmar Sangmo wani wuri ne mai ni'ima. Kafin lokacin da aka fara gudanar da harkokin yawon shakatawa wajen al'adu a shekarar 2002 a kauyen Sangmo, a nan ba ma kawai akwai gonaki masu ni'ima ba, har ma akwai kyakkyawan al'adu masu halayen musamman ciki har wasannin kwaikwayon Tibet da wakokin gargajiya da raye-raye na kabilar Tibet, amma tun dogon lokacin da ya wuce, ba wanda ya gane cewa, irin wadannan kyakkyawan al'adu su ma za su iya kawo musu sauye-sauye wajen tattalin arziki. Mr. Tubdain, direktan kwamitin kauyen Sangmo ya bayyana cewa, "A lokacin da muke yin ayyuka daban-daban, mukan rera wakoki daban-daban, alal misali, lokacin da muke gina gidaje da huda gonaki da kiwon dabbobi, mukan rera wakokin da abin ya shafa. Amma cikin gomomin shekarun da suka wuce, dukkanmu muna aikin noma kawai, ba wanda ya yi tunani cewa, za mu samu kudin shiga ta hanyar rera wakoki da yin raye-raye."

Bisa yunkurin budewar kofa da ake yi a jihar Tibet, mutanen kauyen Sangmo sun fara bunkasa sha'anin noma da ke kewayen birnin Lhasa, ya zuwa shekarar 2002, matsakaicin kudin shiga da kowanen mutum ya samu ya kai kudin Sin wato Yuan 2,500. Wani kamfanin yawon shakatawa na birnin Lhasa ya sa ido kan wannan "Yanki mai daraja" wato kauyen Sangmo, ya yi tattaunawa tare da dagaci ta wancan lokaci mai suna Badro.

Tsohuwar dagaci Badro ta tuna da cewa, a wancan lokaci kamfanin yawon shakatawa ya gaya musu cewa, za a fara gudanar da harkokin yawon shakatawa a kauyensu, amma wannan wani sabon aikin ne a wancan lokaci, shi ya sa da akwai samari 30 kawai da suka yi rajistar yin wannan aiki. Bayan da aka kafa kamfanin yawon shakatawa a kauyen Sangmo, yawan baki masu yawon shakatawa da aka karba a shekarar 2002 ya wuce 2,600, daga baya kuma yawan adalin nan ya yi ta karuwa a kowace shekara, ya zuwa shekarar 2007 kuma, yawan mutane masu yawon shakatawa da aka karba a kauyen Sangmo ya wuce 30,000, matsakaicin yawan kudin shiga da kowanen bakauye ya samu a kowane wata shi ma ya karu daga kudin Sin Yuan 300 na farkon lokaci zuwa Yuan 800 na yanzu.