Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-28 15:43:51    
Kiyaye al'adun al'ummar kasar Sin

cri

Fasahohin al'umma masu daraja da yawa ne suka bace tare da rasuwar tsoffin gwanayen fasahohin ko kuma bacin muhallin da suke rayuwa. Sabo da haka, a shekaru biyu da suka gabata, a hukunce ne "kungiyar kwararrun fasahohin al'umma ta kasar Sin suka fara kama "aikin kiyaye al'adun al'umma". Mashahurin manazarcin al'adun kabilar Naxi kuma mataimakin shugaban kungiyar kwararrun fasahohin al'umma ta kasar Sin Bai Gengsheng ya ce, "A cikin shekarun nan 50 da suka shige, mun taba yin watsi da shi. Yanzu, lokacin da muke raya al'adu masu ci gaba, za mu kara dora muhimmanci a kan ayyukan kiyaye al'adun al'umma daga dukan fannoni, ciki har da matakai da kudi, kuma mun kyautata tsarin aikin nan a wurare daban daban na duk fadin kasar, har ma mun kafa kungiyoyin shugabanni da kwamitocin masana a larduna 26 na kasar. Ban da wannan, yanzu majalisar wakilan jama'ar kasar Sin tana nan tana tattauna maganar kafa dokokin kiyaye al'adun al'umma."

Mr.Bai ya ci gaba da cewa, yanzu kungiyar kwararrun fasahohin al'umma ta kasar Sin tana shirya masana don su tattara fasahohi iri iri na wurare da kabilu daban daban na kasar Sin kuma suna yin bincike a kansu. Bai Gengsheng ya ce, "Muna tattara tatsuniyoyin al'ummar kasar Sin. kuma mun gabatar da ayyukan musamman hudu, wato mun fi mai da hankali a kan al'adun Saman a arewa da al'adun Mazu a gabas da kuma al'adun Nuo a kudu. A yammacin kasar ma, mun fi kulawa da al'adun Tangka."

Manazartan al'adun Sin suna ganin cewa, al'adun al'umma muhimmin kashi ne na al'adun kasar Sin, aikin kiyaye al'adun al'umma da ake aiwatarwa a kasar Sin zai bar wasu al'adu masu daraja a kasar Sin har ma duniya gaba daya. Musamman ma a albarkacin bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin, gwamnatocin wurare daban daban da bangarori daban daban na kasar Sin za su kara shiga cikin aikin nan. A ganin Mr.Bai, ana gudanar da aikin kiyaye al'adun al'ummar kasar Sin da kyau sosai. Ya ce, "kasar Sin tana dora muhimmanci sosai a kan bunkasuwar harkokin al'adu, kuma tana kiyaye al'adun al'umma bisa ma'aunin kasashen duniya da ra'ayi irin na duniya.