Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-27 16:24:26    
An kammala aikin share fage gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing

cri

 

Jiya ran 24 ga wata an kammala gasar Olympics ta yanayin zafi a karo na 29 tare da nasara,gasar Olympics ta nakasassu a karo na 13 za ta fara cikin gaggarumin hali.Za a gudanar da gasar Olympics ta nakasassu ta Beijing daga ran 6 zuwa ran 17 ga wata mai zuwa.A ran 24 ga wata a nan birnin Beijing wani jami'in kwamitin shirin wasannin Olympics na Beijing ya bayyana cewa,ayyukan share fage na gasar Olympics ta nakasassu ta birnin Beijing na tafiya daidai a halin yanzu.Kasar Sin za ta yi kokarin tabbatar da gudanar da gasar Olympics ta nakasassu tare da nasara kamar yadda ta yi da gasar Olympics ta Beijing.

 

A gun taron manema labaran da aka shirya a cibiyar samara da labarai ta duniya ta Beijing ta shekarar 2008,shugaban sashen kula da gasar nakasassu ta kwamitin shirin wasannin Olympics na Beijing Mr Zhang Qiuping ya bayyana cewa,an kawo karshen gasar Olympics a karo na 29 tare da nasara.A ran 25 ga wata birnin Beijing ta shiga wani matakin shirya gasar Olympics ta nakasassu. A cikin kwanaki 12 masu zuwa, birnin Beijing za ta kammala muhimman ayyuka a fannoni guda biyu.

" A wani bangare, kwamitin shirya gasar Olympics na birnin Beijing zai mai da wasu filaye da dakunan wasannni na Olympics da su zama filaye da dakunan wasanni na nakasassu,a wani bangare dabam kuwa zai mai da hankalinsa kan wasu manyan harkoki a birnin."


1 2 3