Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-20 13:57:49    
'Yar wasa ta nahiyar Afirka, wadda ta samu lambar zinariya ta farko a gasar iyo ga Afirka Madam Kirsty Coventry

cri

A ran 16 ga watan Agusta, 'yar wasa ta kasar Zimbabuwei Madam Kirstry Coventry ta samu lambar zinariya a gasar iyon rigingine ta mata ta mita 200 da minti 2 da dakika 5.24, haka kuma ta karya matsayin bajimta na duniya. Lallai, wannan ce lambar zinariya ta farko da 'yan wasa na nahiyar Afirka suka samu a gasannin iyo.

Kafin haka kuma, Madam Coventry ta riga ta samu lambobin azurfa guda uku a gasar wasannin Olympics. Ko da yake wannan lambar zinariya ta zo ne da 'dan makara, amma ta sanya wata kyakkyawar aya ga gasanninta a Beijing. Game da haka, Madam Coventry ta ce,

'A halin yanzu, jikina ya tsumu sosai da sosai. A kwanaki biyu da suka wuce, na sha gasanni sosai, da safe na yi gasar karshe, da yamma kuma na yi wata gasa daban, har ba ni da lokaci da na waiwayi saurin iyona. Yanzu na tuna da abubuwa da dama, wasan iyo ya ba ni sha'awa sosai.'

Kafin shekaru hudu, wato a gasar wasannin Olympics ta Athens, Madam Coventry ta samu lambar zinariya daya, da lambar azurfa daya, da kuma lambar tagulla daya. Bayan da ta koma kasar Zimbabuwei, jama'a sun mayar da ita a wani matsayin jaruma. A wannan karo kuma, sakamakon da ta samu wato lambar zinariya daya da lambobin azurfa 3 za su kara ba da kwarin gwiwa ga 'yan uwanta na kasar Zimbabuwei. Game da haka, Madam Coventry ta ce, 'Na sani, jikin kowa ya tsumu, suna da alfahari da jin wakar kasa ta Zimbabuwei a dakin iyo na 'water cube' mai siffar 'tafkin wanka'. Ina da alfahari sosai da cim ma wannan buri. Ina fatan abubuwan da suka faru a wurin za su kara ba da kwarin gwiwa ga jama'a, za su bayar da tasiri mai kyau gare su.'

Madam Coventry ta ci gaba da cewa, 'A 'yan kwanaki masu zuwa, ni da iyalai za mu huta kadan. Gobe za mu je babbar ganuwa, sa'an nan kuma za mu yi yawon shakatawa a sauran wurare. Ko shakka babu, zan kalli sauran gasannin Olympics, musamman ma gasannin da ban taba ganinsu ba.'(Danladi)