Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-19 19:34:48    
Baki 'yan kasar Nijeriya sun ji dadin wasannin Olympics a Beijing

cri

A ran 8 ga wata, an kaddamar da gasar wasannin Olympics ta lokacin zafi ta karo na 29 a birnin Beijing. Ko da yake akwai matukar nisa tsakanin Sin da Afirka, amma dimbin abokanmu 'yan Afirka sun samu damar zuwan birnin Beijing don jin dadin abubuwan zamani na Beijing da al'adun gargajiya na kasar Sin da kuma halin annashuwa na wasannin Olympics.

"Sannu, Beijing, Nihao. Sunana Vivienne Yusufu, na zo daga kasar Nijeriya. Dukkan 'yan wasanmu mun zo Beijing ne daga kasar Korea ta Kudu ta jirgin sama. Na yi farin ciki sosai da zo nan Beijing domin shiga gasanni. A ganina, tabbas ne zan kece raini a nan, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da ina iya sake samun damar zuwa wannan kyakkyawan birni."

A ran 2 ga watan Agusta da tsakar rana, 'yan wasan Olympics na kasar Nijeriya na rukunin farko sun sauka a filin jiragen sama na kasa da kasa na Beijing. Vivienne Yusufu tana daya daga cikinsu, kuma za ta shiga gasar wasan judo na ajin wadanda nauyinsu bai kai kilo 78 ba. Kuma ta gaya wa wakilinmu cewa, "Beijing wani kyakkyawan birni ne. Na taba zuwa nan a shekara ta 2001, amma ban samu damar duba wannan birni a tsanake ba a wancan karo domin kwanaki kalilan ne na yada zango a nan. Ga shi yanzu na yi sa'a na sake samun damar zuwa nan, inda na kuduri aniyar samun karin ilmi game da wannan birni mai ban mamaki."

Shan bamban da Vivienne, Abdulmalik Ibrahim, wani saurayi dan Nijeriya ne da ya zo Sin don yin balaguro, kuma wannan shi ne karo na farko da ya zo Beijing. Domin wannan ziyara, ya tattara dimbin labarai kan Beijing. Amma lokacin da yake tafiya a manyan titunan Beijing bayan da ya sauko daga jirgin sama, ya ji mamaki sosai da kyawawan abubuwa da ke gaban idonsa. Kuma ya ce, "Lalle Beijing wani birni ne da ke da matukar kyau. An kayatar da ko ina a tsanake, wanda ya wuce abin da nake tsammani a zuciyata. Hausawa su kan fadi cewa:' Gani ya kore ji.' Mutane ba za su fahimci kyan ganin birnin Beijing ba sai dai in sun ganam ma idonsu."

Lokacin da yake yawo a kan titunan Beijing, Kabilu Warkiji da ya zo kasar Sin don yawon shakatawa ya ga kirari "Duniya daya, buri guda" da aka manna a wurare daban daban, wanda aka fassara zuwa harshe iri daban daban. A idonsa, wannan jimla tana da ma'ana sosai. Kuma ya ce, "A ganina, wannan muhimmin take na gasar wasannin Olympics ta Beijing ya dace sosai. A duniyar yau, 'yan Adam suna da buri bai daya, wato hadin gwiwar duk duniya gaba daya. Sabo da haka mutane suna dukufa kan mika zumunci da kauna ta hanyoyi daban daban musamman ma ta wasannin motsa jiki, ta yadda za a iya sa kaimi ga bunkasuwar zamantakewar al'umma da kuma kyautata dangantakar da ke tsakaninsu. A 'yan shekarun nan da suka gabata, kasar Sin ta samu babban ci gaba a fannoni daban daban, kuma ta gasar wasannin Olympics ta Beijing, mutane za su samu damar fahimtar kasar Sin da birnin Beijing, da kuma inganta zumuncin da ke tsakanin jama'ar Sin da jama'ar duniya." (Kande Gao)