Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-18 21:46:52    
An fara aikin gyare-gyare ga dakin ibadan Tashi Lhunpo inda Panchen ke zama da ke jihar Tibet ta kasar Sin

cri

Kwanan baya an fara aikin gyare-gyare ga dakin ibadan Tashi Lhunpo inda Panchen wato shugaban addinin Buddha na Tibet na zuriyoyi daban-daban ke zama, daga cikin ayyukan kiyaye kayayyakin tarihi da ake yi a lokacin shiri na 11 na shekaru 5 na raya kasa a jihar Tibet, gwamnatin tsakiya ta ware kudi mafi yawa domin wannan aiki. Jama'a masu sauraro, yanzu za mu karanta muku cikakken bayani game da wannan labari.

Dakin ibadan Tashi Lhunpo yana gindin tsaunin Nyma da ke arewa maso yammacin birnin Xigaaze na jihar Tibet, fadinsa ya kai murabba'in mita dubu 237, wanda aka gina shi a shekarar 1447, daga shekarar 1713 kuma wannan dakin idaba ya zama wurin da Panchen na zuriyoyi daban-daban ke zama. A cikin dakin ibadan an ajiye kayayyakin tarihi da yawa ciki har da wani mutum-mutumin Buddha mai sunan Qiangba wanda aka sassaka a shekarar 1914 ta hanyar yin amfani da tagulla kuma aka shafe shi da zinari, wanda tsayinsa ya kai mita 26.2, wato shi ne mutum-mutumin Buddha mafi girma a duniyar yanzu. A shekarar 1961, an shigar da dakin ibadan Tashi Lhunpo cikin sunayen kayayyakin tarihin wadanda aka mai da muhimmanci wajen kiyaye su a kasar Sin. Amma sabo da yawan shekarun wannan gini, da dalilin tsarin fasalin ginin da kuma sauye- sauyen yanayi, shi ya sa wannan dakin ibada yana ta lalacewa. Mr. Liu Shizhong, shugaban hukumar kiyaye kayayyakin tarihi ta jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ya bayyana cewa, "Gwamnatin kasar ta ware kudin Sin da yawansu ya kai wajen Yuan miliyan 120 domin aikin gyare-gyare da kuma kiyaye dakin ibadan Tashi Lhunpo, muhimman ayyukan da za a yi suna hade da gyare-gyare ga dakin tunawa da Panchen na zuriya ta 4 da babban dakin mutum-mutumin Buddha mai sunan Qiangba, da kuma aikin tsaro da na kwana-kwana".

Sabo da akwai ayyuka da yawa ga yin wannan gyare-gyare, kuma ana bukatar kudade da yawa domin yin gyare-gyaren, shi ya sa a watan Afril na shekarar 2007, jihar Tibet ta kafa wata karamar kungiyar musamman domin shugabantar wannan aiki. Mr. Xu Xueguang, gwamnan hukumar jihar Xigaaze ya bayyana cewa, cikin gyare-gyaren da ake yi a wannan gami, za a tsaya-tsayin daka ga bin ka'idar "yi wa kayayyakin tarihi gyare-gyare don mayar musu da sigarsu ta zamanin da, kuma ba za a canja asalin tsarinsu ba."

Gyare-gyaren da ake yi ga dakin ibada na Tashi Lhunpo sun samu maraba daga wajen dukkan sufaye da ke wannan wurin ibada, sufi Salung Phunlha, mataimakin direktan kwamitin kula da harkokin zaman yau da kullum na wannan dakin ibada ya yi farin ciki da cewa, "Tabbas ne dukkan sufaye dake cikin dakin idaban Tashi Lhunpo za su rike kulawa da babban taimakon da gwamnatin tsakiya ke nuna musu a zukatansu, kuma za su kara hasken tunanin kare kasa da kawo amfani ga jama'a, da yin biyayya ga nasihohin da Panchen na zuriya ta 10 da ta 11 suka yi musu, kuma za su mai da hankali wajen gudanar da manufar J.K.S. game da addini."

Jihar Tibet tana daya daga cikin larduna da jihohi masu yawan kayayyakin tarihi na kasar Sin, yawan wuraren da ke da kayayyakin tarihi daban-daban wadanda kuma ba za a iya gusar da su ba daga cikin jihar su kai dubbai, daga cikin su da akwai wurare 3 wadanda aka shigar da su cikin sunayen kayayyakin al'adun gargajiya na duniya. Tun daga shekaru na 50 na karnin da ya wuce wato bayan da aka 'yantar da jihar Tibet cikin lumana, musamman ma bayan da kasar Sin ta fara tafiyar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje zuwa yanzu, gwamnatin Sin da ta jiha Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta sun kara rubanya kokari domin ba da kariya ga kayayyakin tarihi, jimlar kudin da aka ware domin wannan aiki ta wuce kudin Sin wato Yuan miliyan 700, bi da bi ne aka gudanar da manyan ayyukan kiyaye kayayyakin tarihi da yawa ciki har da aikin kiyaye da kuma yin gyare-gyare ga fadar Potala na mataki na farko da na 2, haka ma ga dakin ibadan Norbulingka da na Sajia, sabo da haka an sami babban sakamakon kiyaye muhimman kayayyakin tarihi da na al'adun gargajiya na jihar Tibet.