Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-15 15:51:50    
Gasar wasannin Olympic ta dauki alhakin fatan alheri na dukkan al'ummar Japan

cri

Barkanku da war haka, barkanmu da sake saduwa da ku a sabon shirinmu na "Mu leka biranen da suka taba daukar nauyin gasar wasannin Olympic", na babi na birnin Tokyo mai lakabi haka "gasar wasannin Olympic ta dauki alhakin fatan alheri na dukkan al'ummar Japan" Wutar wasannin Olympic ta ci fiye da shekaru 100, ta alamantar da hasken rana da hadin gwiwa da sada zumunci da kwanciyar hankali da adalci, kuma ta kara karfafa zukatan 'yan wasanni na kasa da kasa. Yoshinori Sakai, an haife shi a ran 6 ga watan Agusta a shekarar 1945 watau lokacin da aka yi fashewar boma-bomai na Atom a birnin Hiroshima da ke kasar Japan, abin farin ciki ne, a shekarar 1964, ya kasance mutum mai cunna wuta a gun bikin kaddamar da gasar wasannin Olympic ta Tokyo ta shekarar 1964, kuma yana da ra'ayinsa mai musamman a kan wutar gasar wasannin Olympic. Yau bari mu ji labarin da wakilimmu ya samu daga kasar Japan.

A lokacin da ya dauki nauyin cunna wuta a gun gasar wasannin Olympic ta Tokyo, shekarunsa bai kai 20 da haihuwa ba, yanzu ya riga ya tsufa, a matsayinsa na wani dan wasannin gasar guje-guje da tsalle-tsalle ko da yake bai sami damar shiga cikin gasar wasannin Olympic ba, amma Yoshinori ya shiga cikin gasar wasannin Olympic ta hanyar daban.

"ko da yake daga lokacin da na fara yawo da wuta, zuwa lokacin da na cunna wuta, mintoci uku ne kawai, amma wannan mintoci uku ya canja rayuwata. Sabo da na yi guje-guje cikin wannan mintoci uku, na sami damar sanin sauran mutane masu sana'o'i daban daban, wannan yana da babbar maslaha ga dabi'ata, alal misali, lokacin da na gaza cimma lambobin yabo a gasar wasanni, mutane su ma sun ci gaba da sa ido a kan ni, kuma sun bayar da wasu shawarwari gare ni, kuma abin farin ciki ne, sabo da na sami damar yin mu'ammala tare da sauran mutane masu sana'o'i daban daban, sai na iya gudanar da ayyuka cikin armashi, dukkan wadannan sun yi kamar kadarata".

Game da tasirin gasar wasannin Olympic ke baiwa jama'ar kasar Japan, Yoshinori yana da fahimtarsa.

"Ran 10 ga watan Oktoba, an yi gasar wasannin Olympic ta Tokyo, amma a ranar da ta gabata, an yi ruwa sosai, kowa da kowa ya yi damuwa sosai. Amma a ranar da aka yi gasar wasannin Olympic, an yi rana sosai, yayin da na cunna wuta, sai na ga tufafi na kabilu daban daban na kasa da kasa suna haskakawa a karkashin sararin samaniya, ya zuwa yanzu ban iya mantawa ba. A ganina, gasar wasannin Olympic ta Beijing ba wasannin da aka yi a birnin Tokyo ba, ita ce gasar wasannin Olympic ta dukkan jama'ar Japan. Sabo da, gasar wasannin Olympic ba don sami riba ba ce, ita ce don samun wani abun a zuciyarmu."

A matsayinsa na wani mai tsara labaru wajen motsa jiki, sau da dama, ya kai kasar Sin ziyara, kuma ya taba shiga cikin aikin bayar da labaru wajen gasar wasannin motsa jiki da Sin ta shirya. Yayin da aka tabo maganar gasar wasannin Olympic da za a yi a Beijing, ya bayar da fatan alherinsa.

"Ina fatan gasar wasannin Olympic ta Beijing za ta cimma nasara, Yanzu ana bikin mika wutar wasannin Olympic a wurare daban daban, ina fata za a yi gasar wasannin Olympic cikin kwanciyar hankali"(Bako)