Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-11 15:19:47    
Labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri

---- Biranin Bayannur na jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta ya tsai da shiri cewa, zuwa shekarar 2015 za a shuka takanda cikin gonaki masu fadin kadada dubu 66, yawan makamashin da za a fitar ya kai ton dubu 300 a kowace shekara, ta yadda za a gina wani "sansanin makamashin hallitu" bisa matsayin kasa.

An ce, ba tilas ne a samu yanayin sama da na kasa masu kyau domin shuka takanda ba, kuma ana iya juya shuke-shuke tsakanin dawa da furannin bi rana, sabo da haka ana iya samar da isasshun danyun kayayyaki domin bunkasa makamashin hallitu. Ban da wannan kuma yawan kudin da aka kashe domin fitar da makamashi ton daya daga takandar ba ta wuce kudin Sin Yuan 3,500 ba, wato ana iya tsimin kudi wajen Yuan 1,000 idan an kwatanta shi da na makamashin da aka yi da abinci.

Makamashin halittu ya zama babban makamashi na 4 wato yana bayan makamashin kwal da man fetur da iskar gas kawai. Kasar Sin za ta rubanya kokarinta domin bunkasa makamashin hallitu a kauyuka, ta yadda za a ba da babban taimako domin manufar tsimin makamashi da rage yawan abubuwan kazanta da ake zubarwa.

---- Kwanan baya an fara wani aikin yawon shakatawa wanda aka ware kudin Sin har Yuan biliyan 1.6 domin gina shi a filin ciyayi mafi kayatarwa na jihar Xinjiang da ke arewa maso yammacin kasar Sin. Don haka, yawan kudin da jihar Xinjiang ta kabilar Uighur mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta ware a wannan shekara domin harkokin yawon shakatawa ya wuce kudin Sin Yuan biliyan 14, wato ya wuce dukkan kudaden da aka ware cikin shekaru 10 da suka wuce a wannan fanni.

Ban da wannan kuma, hanyoyin dogon da suka hada kasar Sin da kasar Kirghistan da Uzbekstan, da kuma shirin shimfida hanyoyin dogo, da hanyoyin mota da kuma filayen jigaren sama a cikin jihar Xinjiang dukkansu sun aza harsashi mai kyau domin kyautata ingancin harkokin yawon shakatawa na jihar Xinjiang.

Bisa kididdigar da aka yi an ce, daga watan Janairu zuwa watan Yuni na wannan shekarar da muke ciki, jimlar baki masu yawo shakatawa da jihar Xinjiang ta karba ta wuce miliyan 8.7, jimlar kudin da ta samu daga harkokin yawon shakatawa kuma ta wuce kudin Sin Yuan biliyan 7.