Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-11 15:17:06    
Ziyarar da kananan manzannin kabilu 56 suka yi dangane da wasannin Olimpic

cri

Kwanan baya, bisa gayyatar da kwamitin shirya wasannin Olimpic na Beijing ya yi musu ne, kananan manzannin kabilu 56 suka kawo ziyarar a nan birnin Beijing dangane da wasannin Olimpic. Cikin shirinmu na yau na "kananan kabilun kasar Sin", za mu kawo muku bayani game da ziyarar da wadannan kananan manzannin suka yi dangane da wasannin Olimpic.

Daga cikin wadannan kananan manzannin kabilu 56, wanda ya fi girma shekarunsa 15 ne, wanda ya fi karami kuwa shekarusa 8 ne kawai, dukkansu sun zo ne daga lardin Sichuan da jihar Tibet da ta Xinjiang na kasar Sin. Daga cikin su kuma, da akwai yara 2 'yan kabilar Qiang wadanda suka zo daga yankin Aba na shiyyar da bala'in girgizar kasa ya shafa da ke lardin Sichuan, gidajensu sun rushe sabo da mummunar girgizar kasa da ta auku a ran 12 ga watan Mayu a gundumar Wanchuan ta wannan lardi, amma duk da haka, suna nuna karfin zuciya da farin ciki a gaban mutane. Yarinya Chen Gulu, 'yar kabilar Qiang da ta zo daga lardin Sichuan ta ce,

"Ina fatan ni da dukkan kananan aminaina wadanda ba su taba zuwa Beijing ba, za su iya samun damar zuwan nan Beijing domin kallon wasannin Olimpic a ranar bikin bude wasannin."

Bayan da karamin manzon kabilar Tong mai sunan Yang Xinxin wanda ya zo daga lardin Guizhou ya ziyarci filin wasan motsa jiki na kasa mai siffar "sheka", ya bayyana cewa,

"A ganin na, siffar filin wasan motsa jiki na kasa ta kasance tamkar wata sheka da tsuntsaye suka gina ta hanyar cafki rassan itatuwa da bikunansu, lalle tana da kyaun gani."

Ban da filin wasan motsa jiki na kasa mai siffar sheka da wurin wasan da ake kira "Water Cube" wato cibiyar wasan iyo ta kasar Sin, kuma wadannan kananan mazannin sun je cibiyar wasannin motsa jiki ta nakasassun kasar Sin da ke nan birnin Beijing don yin musanyar ra'ayoyinsu da kara wa junansu ilmi. Karamin manzon kabilar Yi mai sunan Yang Xiaohua wanda ya zo daga lardin Sichuan ya yi farin ciki da cewa,

"Sabo da a garinmu babu filin wasan kwallon kafa irin haka, shi ya sa na yi farin ciki sosai da na samu damar zuwan nan a yau don yin ziyara."

A rana ta karshe ga yin ziyarar, hukumar da ta shiya wannan ziyara kuma ta shirya wani bakin gama ziyarar domin wadannan kananan manzannin kabilu 56 da suka zo ziyara a nan birnin Beijing dangane da wasannin Olimpic. A gun bikin, kananan manzannin sun sa kayan salla na kabilunsu, sun yi wake-wake da raye-raye don su bayyana kauna ga zaman rayuwarsu ta hanyar yin raye-raye, da bayyana burin tabbatar da mafarkinsu ta hanyar yin wake-wake da muryoyin yara. A gun bikin kuma, yarinya Dong Fang, 'yar kabilar Jinuo ta rera wata wakar da uwarta ita kanta ta koya mata, sunan wakar shi ne, "Kauyukan tudun Jinuo suna nuna maka maraba", kuma ta gayyaci sabbin aminanta da ta kulla aminci tare da su a nan birnin Beijing za su kai ziyara a garinta. Ta ce,

"Na yi farin ciki da na kai ziyara cikin 'yan kwanakin nan da suka wuce a nan birnin Beijing, kuma na kulla aminci tare da aminai da yawa, ina fatan wadannan aminaina za su iya kai ziyara a kauyukan dutun Jinuo na garinmu."

Ko da yake an gama ziyarar da kananan manzannin kabilu 56 suka yi dangane da wasannin Olimpic, amma ziyarar ta ba wadannan kananan manzanni zurfaffiyar alama a zukatansu. Dalilin da ya sa haka shi ne domin wannan ya zama karo na farko ke nan da suka zo nan birnin Beijing, kuma karo na farko ne da suka samu damar kai ziyara a filin wasan motsa jiki na kasa mai siffar sheka da wurin wasan da ake kira "Water Cube" wato cibiyar wasan iyo ta kasar Sin, karo na farko ne da suka je kallon bikin daga tutar Sin da aka yi a babban filin Tiananmen, kuma karo na farko ne da suka ci abincin Macdonald, shi ya sa ana iya tabbatar da cewa, ba shakka ziyarar da suka yi a wannan gami za ta rubata wani shafi mai daraja cikin duk zaman rayuwarsu.