Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-05 19:23:27    
Birnin Beijing yana maraba da zuwan gasar wasannin Olympics ta Beijing bisa harkokin al'adu iri daban daban

cri

Abin da kuke saurara shi ne wata waka mai taken "Addu'ar da aka yi wa gunkin rana wato Apollo", wadda mace mai wa'azi ta kasar Greece da ta taba kunna wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing ta karanta a babban dakin taruwar jama'a na birnin Beijing. Tare da muryarta mai dadin ji, an kaddamar da bikin fasaha na karo na shida na wasannin Olympics kuma bikin harkokin al'adu na shekara ta 2008 wato 'gamuwa a birnin Beijing'.

Kuma wannan ya shaida cewa, daga watan Yuni na shekarar bana har zuwa watan Satumba wato bayan da aka kammala gasar wasannin Olympics ta nasakassu, za a shirya bukukuwan fasaha sau biyu ko uku a ko wace rana a birnin Beijing ta hanyoyi iri daban daban. Kungiyoyin fasaha sun zo daga kasashe da yankuna fiye da 80, kuma yawan kwararrun da suka sa hannu a cikin bukukuwan zai kai fiye da dubu 20. Ban da wadannan bukukuwan fasaha fiye da 260 da za a yi a cikin daki, a sa'i daya birnin Beijing zai shirya manyan nune-nune 160 na gida da na waje.

Kamfanin kula da ayyukan nuna wasannin fasaha a ketare na kasar Sin yana kula da aikin shigad da nune-nunen wasannin fasaha cikin kasar Sin. Zhang Yu, babban manaja na kamfanin ya bayyana cewa, sun riga sun yi shiri har fiye da shekara guda, suna fatan za a iya nuna ire-iren al'adun duniya sosai ta wannan harka. Kuma ya kara da cewa,

"Gasar wasannin Olympics wani biki ne na duk duniya. Ta hanyar koyon sakamako mai kyau da kasashe daban daban suka samu kan shirya harkokin al'adu na wasannin Olympics, mun tattara kungiyoyin fasaha da ayyukan fasaha mafi nagarta na duk duniya domin jin dadin al'adun kasashen duniya tare."

Idan za a iya jin dadin kyawawan fasahohi na duniya ta hanyar kallon bukukuwan fasaha, to tabbas ne za a iya ganin yadda Sinawa ke nuna wa gasar wasannin Olympics kauna ta harkokin al'adu na fararen hula na birnin Beijing. Madam Wangzhu, kakakin hukumar al'adu ta birnin Beijing ta bayyana cewa, "An gina filayen al'adun wasannin Olympics 26 a birnin Beijing gaba daya, a ciki, fadin babban fili ya kai murabba'in mita dubu gomai, wanda ke iya daukar mutane fiye da dubu goma, karamin fili kuma yana iya daukar mutane fiye da dubu guda. A wadannan filaye, mutane suna iya jin dadin wasannin Olympics har kwanaki 66, kuma fiye da sa'o'i 8 a ko wace rana. Ban da wannan kuma za a shirya nune-nune kan al'adu da tarihin wasannin Olympics da kuma abubuwan tarihi na al'adu na kasar Sin da aka gada daga kakanni zuwa kakanni."

1 2